Mbappe na jin PSG ta yi masa ''romon baka'' zai bar kungiyar a Janairu

Asalin hoton, Getty Images
Kylian Mbappe na jin cewar Paris St Germain ta ''yaudare shi'' yana son barin kungiyar a watan Janairu in ji Julien Laurens mai sharhin tamaula a Faransa.
A watan Mayu dan kwallon tawagar Faransa ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda kaka uku a PSG, amma yanzu yana jin ya yi ''kuskure''.
Mbappe, wanda ya ci kwallo 12 a dukkan wasan da ya yi wa PSG a bana na son komawa taka leda Real Madrid.
Sai dai daraktan wasanni na PSG, Luis Campos ya ce dan kwallon mai shekara 23 bai taba cewar zai bar kungiyar a Janairu ba.
A hirar da aka yi da shi a BBC Radio 5 kai tsaye, Laurens ya ce ''Sun yi masa alkawarin za su sayo mai cin kwallo, domin ya koma buga gurbin da yafi kauna, za a sayar da Neymar - za su dauki mai tsaron baya daga tsakiya, sannan shi ne zai ke jagorantar dukkan abin da za a yi a kungiyar.
Sai dai ba alkawarin da aka cika masa.
''Mun san cewar akwai rudani a wannan lokacin, amma yanzu ya yanke shawarar baya son ci gaba da zama a PSG. yana kuma jin yayi kuskure da ya amince ya tsawaita kwantiraginsa, wanda ya kamata ya koma wata kungiyar kan fara kakar bana, yanzu yana duba inda ya kamata ya koma idan an bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo a watan Janairu.''
Mbappe wanda ya lashe kofin duniya da Faransa a Rasha a 2018 ya dauki kofi 11 a PSG har da Ligue 1 hudu, tun bayan da ya koma kungiyar daga Monaco a 2017, wanda ya fara da wasanin aro.
Ranar Juma'a mujallar Forbes ta bayyana shi a matakin wanda ke kan gaba a samun kudin shiga a duniya a 2022 tsakanin masu taka leda - karon farko da Lionel Messi ko Cristiano Ronaldo da suke rike gurbin.












