Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sojojin Najeriya sun kashe ƴan bindiga bakwai a Kaduna, sun 'kama kwamandan ISWAP' a Neja
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kashe ƴan bindiga bakwai a Jihar Kaduna tare da ƙwato makamai.
Haka kuma wasu rahotannin na cewa sojojin sun daƙile wani hari da aka kai musu a wani sansanin su da ke Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja har sun kama kwamandan ƙungiyar ISWAP.
A wani saƙo da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebbok, ta bayyana cewa tun da farko dakarun Operation Safe Forest Sanity ne suka ƙaddamar da wani samame a Maidaro da Tudun Kagi da Kusharki da kuma Anguwan Madaki duka da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari.
A yayin samamen, sojojin sun yi musayar wuta da ƴan bindigar inda suka kashe ƴan bindigar huɗu tare da ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu da lodi biyu na harsasai samfarin 7.62mm da kuma bindiga ƙirar Pump Action ɗaya da harsasai uku da ƙananan bindigogi na gargajiya uku da babura huɗu.
A wani samamen da sojojin kuma suka kai a ƙarƙashin runduna ta ɗaya ta sojojin Najeriyar, dakarun sun kai samame a yankunan Sabon Birni-Zartake da Ungwan Lima Riyawa da Tungan Madaki inda sojojin sama suka taimaka domin yin ƙofar rago ga ƴan bindigar da ke tserewa daga Tudun Kagi.
Rundunar ta ce bayan musayar wuta, an kashe ƴan bindigar har uku.
Bayan haka kuma gidan talabijin na Najeriya ya ruwaito cewa sojojin sun daƙile wani hari da aka kai bataliya ta 221 da ke New Bussa a Karamar Hukumar Borgu, amma sojoji sun daƙile harin.
Wasu rahotanni kuma sun ce sojojin sama ne suka taimaka wa dakarun da ke sansanin domin fatattakar maharan.
Haka kuma Jaridar PR Nigeria ta ƙasar ta ce a yayin daƙile wannan harin, sojojin Najeriya sun samu nasarar kama wani kwamanda na ƙungiyar ISWAP, duk da cewa har zuwa yanzu sojojin ba su tabbatar da hakan ba.