Damben Dan Aliyu da Rabe bai yi gwani ba a Maraba

Damben gasa tsakanin Dan Aliyu da Rabe sun tashi canjaras ranar Lahadi a gidan wasa na Idris Bambarewa da ke jihar Nasarawa a Najeriya.
Bayan da Labaran dan Gwamba ya yi musu kida masoya suka yi musu alheri, sai suka shiga tsakiyar fili, inda alkalin wasa Anas Dandume ya daga hannunsu.
Nan da nan suka fara wasa mai zafi a tsakaninsu, inda Dan Aliyu daga Jumus da Rabe Bahagon Ebola daga Kudu kowa ya nuna kwazonsa.
Koda yake turmi daya suka buga aka raba su, bayan da Rabe Bahagon Ebola hannunsa ya tashi, daga nan aka tashi daga fafatawar.
Tun farko an fara da damben gasa tsakanin Ushu Shagon Inda daga Arewa da Autan na Aisha Guramada, wanda yanzu wata biyar yana tsaye bai fadi ba.
Damben na su turmi uku suka yi har da karin lokacin, amma bai yi gwani ba, kuma wasan bai wani kayatarba, kamar yadda aka sa ra tun makon jiya.
Sakamakon wasannin da aka yi kisa:
- Bahagon Autan Mamman ya buge Shagon Bahagon Ali Yaro
- Boloko ya buge Dankwalle
Sakamakon wasannin da aka yi canjaras:
- Bahagon Kurma da 'Yar Mage
- Korona da Shagon Lawwalin Gusau
- Autan Makada da Autan Sanin Gidan Dan Kande
- Dan Butsallee da Bahagon Dan Aliyu
- Dan Bichi da Na Dada











