Manchester United: Erik ten Hag da Rashford sun lashe kyautar koci da dan wasan watan Satumba

An wallafa

Kocin Manchester United Erik ten Hag da dan wasansa Marcus Rashford sun lashe kyautar koci da dan wasan da suka fi kowa kokari a watan Satumba.

Ten Hag mai shekara 52, ya yi rashin nasara a wasanninsa biyu na farko bayan barin Ajax, bayan nan kuma sai da ya samu nasara hudu a jere a Premier.

Nasarar da ya samu kan Liverpool da Southampton a watan Agusta ta ci gaba har zuwa wadda ya yi a kan Leicester City da Arsenal.

Marcus Rashford dan shekara 24, shi ne ya ci Arsenal kwallo biyu abin da ya karara rura wutar nasarar United.

Ten Hag ya zama koci na biyu tun bayan barin Sir Alex Ferguson kungiyar, da ya lashe wannan kyauta, bayan Ole Gunnar Solskjaer da ya lashe a watan Janairun 2019.

Hukuncinsa na mayar da Rashford ya rika bi ta tsakiya na daya daga cikin abubuwan da suka rura wutar kokarin Manchester United.

Dan wasan gaban Ingilan wanda bai samu damar buga wasannin kasashe da aka yi ba saboda raunin da ya ji, ya bai wa Jadon Sancho kwallon da ya ci Leicester wadda ita ce guda, sai kuma wadda ya bai wa Anthony ya fara cin Arsenal a wasan da aka tashi 3-1.

"Watan Satumba na cikin lokutan tarihin da ba zan manta da su ba a rayuwata," in ji Rashford.

"Kwallon da Anthony ya fara ci a wasansa na farko. Ta faranta mana kuma ta kara mana kwarin gwiwa da karsashi. Ganin shi a kungiyar da kuma cin kwallo a wasa mai mahimmanci irin wannan."

Rashford, ya ci kwallo a wasansu da Liverpool a watan Agusta, inda ya ci dan wasan da ya fi kokari a watan tun wadda ya ci a watan Janairun 2019. Nasarar United ta fara ne bayan da ta farfado daga kasan teburin Premier bayan rashin nasarar da ta yi a wasanni biyu, ta kuma yi nasara a wasanni biyar.

Sun buga wasa biyu ne kawai a watan Satumba bayan dage wasansu da aka yi da Crystal Palace da Leeds United saboda mutuwar Sarauniya Elizabeth II.