Newcastle ta yi watsi da tayi kan Trippier, Casemiro na cikin rashin tabbas a Man Utd

Asalin hoton, Getty Images
Newcastle United ta yi watsi da tayin Bayern Munich kan dan wasanta mai shekara 33 Kieran Trippier. (Sky Sports)
Trippier ya nuna matukar damuwar komawa Bayern a wannan Janairun idan aka cimma yarjejeniya da kungiayarsa. (Times - subscription required)
Newcastle ta kuma yi watsi da tayin tafiya zaman aro kan dan wasan Ingila Callum Wilson daga Atletico Madrid ammma tana iya sayar da shi kan yarjejeniyar dindindin. (Mail)
Tsohon kocin Chelsea da Manchester United Jose Mourinho na tattaunawa da Al-Shabab ta Saudiyya. (Sportitalia - in Italian)
Ɗan wasan baya a Brazil Casemiro ya shiga rashin tabbas kan makomarsa a Manchester United idan kakar nan ta kare bayan da kungiyar ke ganin cewa abu mafi dacewa shi ne ta cefanar da shi. (Star)
Kocin Manchester United Erik ten Hag na hanzarin ganin cewa ya dauko ɗan wasan Ajax, mai shekara 21 Brian Brobbey. (Sky Sports Germany)
Matthijs de Ligt na shirin barin Bayern Munich a wannan kaka a daidai lokacin da Manchester United ta nuna tana son ɗan wasan mai shekara 21. (Mirror)
Ɗan wasan Sifaniya, Aymeric Laporte da ya bar Manchester City zuwa Al-Nassr a kakar da ta gabata ya ce akwai 'yan wasa da dama da ba sa jin dadin zamansu a Saudiyya. (AS - in Spanish)
Ɗan wasan gaba a RB Leipzig da Slovenia, Benjamin Sesko mai shekara 20, da na damar barin ƙungiyar kan fam miliyan 43 kamar yada yake kunshe a yarjejeniyarsa daga wannan kaka. (Sky Sports Germany)
Everton za ta jinkirta kan ɗan wasan Mali mai shekara 31, Abdoulaye Doucoure, da ke alakantawa da ƙungiyar Al-Ettifaq ta Saudiyya a kokarin maye gurbin Jordan Henderson na ingila mai shekara 33, da ya je Ajax. (Liverpool Echo)
Newcastle da Borussia Dortmund na kokarin saye ɗan wasan Faransa mai shekara 18 Desire Doue daga Rennes. (L'Equipe - in French)
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya sanyaya gwiwar magoya-bayansu a cinikin saye ɗan wasan Brentford mai shekara 27, Ivan Toney. (Mirror)
Aston Villa ta gabatarwa Middlesbrough sabon tayi kan ɗan wasanta mai shekara 21, Morgan Rogers. (Fabrizio Romano)
Manchester City na son kawo ɗan wasan Brazil Savio da ke zaman aro a Girona daga Troyes.(Star)











