Najeriya ta yi canjaras da Saudi Arabia a wasan sada zumunta

Super Eagles

Asalin hoton, NFF/X

An wallafa

Najeriya ta tashi kunne-doki 2-2 a wasan sada zumunta da ta buga da Saudiyya a filin wasan Estádio Municipal de Portimão da ke ƙasar Portugal.

Salman Al-Faraj ya fara jefa ƙwallo a ragar Najeriya a minti na 60 da fara wasa, amma Najeriya ta farke a minti na 73 lokacin da Abdulelah Al-Amri ya ci gida bisa kuskure.

Kelechi Iheanacho ya ƙara wa Najeriaya ƙwallo ta biyu a minti na 81 wanda hakan ya kusa tabbatar mata da nasara a wasan kafin Mohamed Kanno ya farke ma Saudiyya a cikin ƙarin lokaci.

A wasanta na gaba Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da da Mozambique a ranar 16 ga wannan watan a inda ita kuma Saudiyya za ta ƙara da Mali.

A sauran wasannin sada zumunta da aka buga ranan Juma'a Japan ta doke Kanada da ci 4-1 a inda Korea ta lallasa Tunisia da ci 4-0.

Wasan da aka buga tsakanin Qatar da Iraƙi ya ƙare babu ci amma Qatar ta yi nasara da ci 6-5 a bugun fenariti a inda shi ma wasan Afirka ta Kudu da Eswatini ya ƙare 0-0.