Wasannin da Real Madrid za ta yi a cikin watan Janairu

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid za ta buga wasa bakwai a gasa huɗu a cikin watan Janairun 2025.

Watakila ta yi karawa tara idan ta kai zagayen gaba a Copa del Rey da zuwa wasan karshe a Spanish Super Cup.

Ƙungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama za ta fara da wasa na La Liga ranar 3 ga watan Janairu da Valencia.

Kwantan wasa ne da ya kamata su buga cikin 2024, amma aka sako sakamakon ambaliyar ruwa da ya shafi Sifaniya.

Kwana uku tsakani Real za ta fara Copa del Rey zagayen ƴan ƙungiya 32 da za ta ziyarci Deportiva Minera.

Ranar 9 ga watan Janairu, Real Madrid za ta yi wasa na uku a sabuwar shekara a Spanish Super Cup zagayen daf da karshe da Mallorca.

Idan har Real Madrid ta kai zagayen gaba a gasar, za ta yi wasan karshe ranar 12 ga watan Janairu a Saudi Arabia.

A mako na uku da shiga 2025 za a ci gaba da fafatawar Copa del Rey, fafatawa tsakanin ƙungiyoyi16 da za a kara tsakanin 15-16 ga watan Janairu.

Ranar Lahadi 19 ga watan Janairu za a koma buga La Liga wasan mako na 20, inda Real Madrid za ta ƙarbi bakuncin Las Palmas.

Kwana uku tsakani Real za ta buga Champions League da Salzburg, daga nan za ta yi gumurzu biyu a waje kafin watan Janairu ya kare.

Kenan za ta je Valladolid ranar 25 ga watan Janairu a La Liga, sannan ta karkare da wasa a gidan Brest ranar 29 ga watan Janairu a babbar gasar zakarun Turai.

Wasannin da Real Madrid za ta yi a cikin watan Janairu:

  • -Valencia da Real Madrid ranar 3 ga watan Janairu
  • -Deportiva Minera da Real Madrid ranar 6 ga watan Janairu
  • -Real Madrid da Mallorca ranar 9 ga watan Janairu
  • -Real Madrid da Las Palmas ranar 19 ga watan Janairu
  • -Real Madrid da Salzburg ranar 22 ga watan Janairu
  • -Valladolid da Real Madrid ranar 25 ga watan Janairu
  • -Brest-Real da Madrid ranar 29 ga watan Janairu