An sanar da ranar da za a kara tsakanin Barca da Real a La Liga

El Clasico

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

An tsayar da ranar da za a buga wasa tsakanin Barcelona da Real Madrid a wasa na biyu a La Liga, wato karawar El Clasico.

Za a buga wasan ne ranar 11 ga watan Mayu wato fafatawar mako na 35 a La Liga a filin wasa na Estadi Olímpic Lluís Companys

Barcelona tana mataki na ɗaya kan teburin La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Real Madrid ta biyu mai rike da kofin bara.

Wasan da Barcelona za ta yi kafin ta fuskanci Real a La Liga:

Champions League ranar Talata 15 ga watan Afirilu

  • Borussia Dortmund da Barcelona

La Liga ranar Asabar 19 ga watan Afirilu

  • Barcelona da Celta Vigo

La Liga ranar Talata 22 ga watan Afirilu

  • Barcelona da Mallorca

Copa del Rey ranar Asabar 26 ga watan Afirilu

  • Barcelona da Real Madrid
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

La Liga ranar Lahadi 4 ga watan Mayu

  • Valladolid da Barcelona

Wasannin da Real za ta kara kafin ta fuskanci Barca a La Liga:

Champions League ranar Laraba 16 ga watan Afirilu

  • Real Madrid da Arsenal

La Liga ranar Lahadi 20 ga watan Afirilu

  • Real Madrid da Ath Bilbao

La Liga ranar Laraba 23 ga watan Afirilu

  • Getafe da Real Madrid

Copa del Rey ranar Asabar 26 ga watan Afirilu

  • Barcelona da Real Madrid

La Liga ranar Asabar 3 ga watan Mayu

  • Real Madrid da Celta Vigo

Karo na uku kenan da za a fafata a wasan na El Clasico a bana:

Barcelona ta yi nasara sau uku a kan Real Madrid a bana, inda ta fara cin 2-1 a New York a wasannin atisayen tunkarar kakar nan.

Na biyu shi ne 4-0 da Barcelona ta caskara Real Madrid a La Liga ranar Lahadi 26 ga watan Oktoban 2024 a Santiago Bernabeu.

Wasa na uku shi ne wanda Barcelona ta lashe Spanish Super Cup a Saudi Arabia, bayan nasara a kan Real Madrid da cin 5-2.

Shi ne kofin farko da Hansi Flick ya ci a Barcelona a kakar farko da ya fara jan ragamar Barcelona, wadda ta yi wasa 24 a jere ba a doke ta ba a dukkan fafatawa.

Rabon da Barcelona ta yi rashin nasara tun cikin Disambar 2024, bayan da Atletico Madrid ta je ta ci 2-1 a La Liga.

Manyan ƙungiyoyin za su fafata a Copa del Rey ranar 26 ga watan Afirilu daga nan kowacce za ta yi wasan La Liga, sai su kara fuskantar juna a babbar gasar tamaula ta Sifaniya .

Kenan karo huɗu za a buga El Clasico a kakar nan ko kuma biyar da zarar Barcelona da Real Madrid sun kai wasan karshe a Champions League a bana.

A gasar bara a La Liga, Real Madrid ta yi nasara a kan Barcelona da cin 2-1 a Estadi Olímpic Lluís Companys, saboda haka komai zai iya faruwa da zarar sun haɗ a cikin watan Mayu.