Osasuna za ta kara shigar da Barca kara kan amfani da Martinez

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

An kori kakar da Osasuna ta shigar da Barcelona kan amfani da ta yi da mai tsaron baya, Inigo Martinez a lokacin gasar La Liga.

Sai dai Osasuna ta ce za ta kara shigar da kara, ba ta amince da hukuncin ba, bayan da Martinez bai yi wa tawagar Sifaniya wasa ba, sakamakon raunin da yake jinya.

A dokar Fifa ba a amince ɗan wasa ya buga wa ƙungiyarsa tamaula kwana biyar tsakani ba, har sai idan hukumar ƙwalllon kafar kasar ta amince ya je ya buga wasa, ko kuma bai halarci sansanin da tawagarsa ta gayyace ba.

Barcelona ta doke Osasuna 3-0 a kwantan wasa da ya kamata su kara ranar 8 ga watan Maris, amma aka soke saboda mutuwar likitan ƙungiyar Carles Minarro.

Sun kuma yi karawar a tsakaninsu, kwana ɗaya da kammala wasaninin kasa da kasa da Fifa kan ware, kenan kwana huɗu tsakani da Sifaniya ta yi nasara a kan Netherlands a Uefa Nations League.

Martinez ya buga wa Barcelona wasan da ta doke Osasuna tsawon minti 90 a fafatawar da suka yi ranar 27.

Osasuna ta shigar da kara kwana ɗaya tsakani da ta fuskanci Barcelona ga hukumar ƙwallon kafa ta Sifaniya.

To sai dai hukumar ƙwallon kafar Sifaniya ta sanar ta kwamitin da ta kafa cewar Martinez bai karya ka'ida ba, ya bi dukkan hanyar da ta dace kan komawa Barcelona.

To sai dai Osasuna ta ce za ta kara shigar da kara karo na biyu ga kwamitin na hukumar ƙwallon kafar Sifaniya.

Barcelona tana matakin farko a teburin La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Real Madrid ta biyu, ita kuwa Osasuna tana mataki na 13.