An kashe mutum 19 a harin da aka kai fadar shugaban ƙasar Chadi

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a ƙasar Chadi sun ce jami'an tsaron ƙasar sun daƙile wani hari na ƙoƙarin haifar da ruɗani a ƙasar.
A daren ranar Laraba ne wani gungun ƴan bindiga ya far wa fadar shugaban ƙasar da ke N'Djamena, babban birnin ƙasar.
Ministan harkokin wajen ƙasar, Abdel Rahmane Koulamallah ya ce, "mun daƙile yunƙurin jefa ƙasarmu cikin ruɗani, yanzu komai ya koma yadda yake.
"An kashe maharan 19 da soja ɗaya, shida kuma sun samu rauni."
Tuni aka jibge jami'an tsaron a duk hanyoyin babban birnin ƙasar, tare da jigbe tankokin yaƙi a kusa da fadar gwamnatin ƙasar.
Sai dai mazauna babban birnin sun ce zai yi wahala a iya far wa gwamnatin Chadi gaba da gaba saboda sun yarda da ƙarfin sojin ƙasar.
"A matsayina na mazaunin N'Djamena, ko gezau ba na shakkar ƙarfin sojin Chadi.
Bidiyon da muka gani sun nuna cewa an kashe maharan, kuma an kama wasu.
''Akwai tashin hankali a labarin, saboda ba mu san me zai biyo baya ba," in ji wani mazaunin ƙasar wanda ba ya so a bayyana sunansa.
Wata majiya ta kusa da gwmanatin ƙasar ta ce jami'an tsaron ƙasar sun gwabza da "wasu ƴan ta'adda"
A watan jiya ne aka gudanar da zaɓen majalisar ƙasar Chadi, zaɓen da ƴan adawa suka yi kira ga magoya bayansu su ƙaurace masa saboda zargin za a tafka maguɗi.
Mahamat Idriss Déby dai maye gurbin mahaifinsa Idriss Déby, wanda aka kashe bayan ya yi kusan shekara 30 yana mulkin ƙasar.
A watan Nuwamba ne ƙasar Chadi ta kawo ƙarshen yarjejeniyar aikin soji da ke tsakaninta da Faransa, inda ta buƙaci sojojin ƙasar wadda ta raine ta su fice.
Yanke alaƙar sojin ya zo ne a daidai lokacin da ake cigaba da musayar yawu bayan ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar sun raba-gari da ƙasar ta Faransa.
Haka kuma ƙasashen Senegal da Ivory Coast duk sun buƙaci Faransa ta kwashe sojojinta a ƙasarsu.










