Iran ta sanar da dakatar da kai hare-hare kan Isra’ila

Asalin hoton, Getty Images
Hedikwatar Khatam al-Anbiya ƙarƙashin rundunar juyin juya halin Iran ta fitar da wata sanarwa da ke bayyana cewa ta kawo ƙarshen hare-haren da ta ke kai wa kan Isra’ila.
Sanarwar ta bayyana cewa dalilin hare-haren Iran kan Isra'ila shi ne ci gaba da hare-haren da take kai wa a kudancin Lebanon da yankin Dahiya.
Hedikwatar ta ce ta mayar da “martani mai zafi” kan Isra’ila domin goyon bayan al’ummar Lebanon da ke cikin wahala, tare da cewa bisa haka aka yanke shawarar dakatar d akai hare-haren.
Sai dai ta gargaɗi cewa idan har hare-haren Isra’ila suka ci gaba, musamman a kudancin Lebanon, za a ɗauki “tsauraran matakai masu tsanani fiye da yadda ta yi a yanzu.”





















