Me ya jawo saɓani tsakanin Faransa da Chadi kuma me zai biyo baya?

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Armand Mouko Boudombo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Afrique
- Aiko rahoto daga, Dakar
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
A ranar Alhamis, Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noël Barrot ya amsa kiran waya daga Shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby Itno.
A daidai lokacin da Barrot yake ziyarar aiki a ƙasar ne kuma Chadi ta sanar da cewa za ta yanke alaƙar harkokin soji ta gomman shekaru tsakaninta da Faransar.
Faransa ce ƙasar da ta yi wa Chadi mulkin mallaka, wanda hakan ya sa yanke alaƙar ta jawo tambayar ko dai ƙarfin ikon Faransa ne ke ƙara samun tangarɗa a yankin Sahel.
Alaƙar harkokin soji tsakanin ƙasashen biyu ta samo asali ne daga wata yarjejeniya da ta kwashe kusan shekara 50. Faransa ta sake saka hannu kan yarjejeniyar bayan an yi mata garambawul a shekarar 2019.
Amma Shugaban Ƙasa Mahamat Idriss Deby ya shaida wa Minista Barrot cewa zai rushe yarjejeniyar.
Ministan harkokin wajen Chadi, Abderahmane Koullamala, ya ce gwamnatin ta yanke shawarar ɗaukar matakin ne bayan "nazari mai zurfi."
Ya ce wannan na cikin yunƙurin ƙasar ta Chadi "domin cin gashin kanta 100 bisa 100, tare da sake tsara yarjejeniya daban-daban da take ciki domin sanya manufufi da muradun ƙasar a gaba".
Sai dai gwamnatin Chadi ta ce yanke alaƙar sojin ba zai shafi alaƙar diflomasiyya ba, sannan ƙasar za ta bi doka wajen yanke alaƙar sojin cikin tsari.

Asalin hoton, AFP
Chadi ta ɗauki wannan matakin ne bayan ofishin babban mai gabatar da ƙara na Faransa ya ƙaddamar da bincike kan almundahana da sace kuɗin al'umma.
Ofishin mai gabatar da ƙarar ya yi zargin cewa Shugaban Deby ya yi amfani da kusan fan 900,000 (CFA miliyan 580) domin sayen ɗarurwan riguna na alfarma a Faransa.
Waɗannan zarge-zargen sun ƙara ɓata alaƙar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.
Wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Seidik Abba, ya yi amannar cewa yunƙurin fara binciken na cikin abubuwan da suka lalata alaƙar, wadda ta kasance mai kyau a baya.
Ya ce lamarin ya ƙara fitowa fili ne a lokacin da Faransa ta ƙi shiga wani aikin soji na musamman da aka yi a ƙasar domin yaƙi da ƙungiyar Boko a yankin tafkin Chadi.

Asalin hoton, Reuters
Me ke faruwa yanzu?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Chadi na da matuƙar muhimmanci a yaƙin da ƙasashen yamma ke yi da ƙungiyoyi masu ikirarin jihadi a yankin Sahel na Afirka ta yamma.
Kafin zaɓen shugaban ƙasar a watan Mayu, hukumomi a ƙasar Chadi sun buƙaci sojojin Amurka su fice daga ƙasar.
Yanzu haka akwai sojojin Faransa aƙalla 1,000 a ƙasar Chadi, waɗanda suke taimakon ƙasar wajen tattara bayanan sirri da kai ɗauki ga sojojin na Chadi daga sansanoninsu da suke cikin ƙasar, har da a birnin N’Djamena.
Akwai sansanonin sojojin Faransa a barikin sojojin sama na 172 Airbase da ke Ndjamena da wani a sansanin Captain Croci da ke Abéché, da ke gabashin ƙasar, da waɗanda suke Faya-Largeau da ke arewaci, kuma ana tunanin dukkansu za su bar ƙasar.
Sojojin sun taimaka a lokuta da dama, musamman wajen hana ƴan tawaye samun damar kutsawa cikin ƙasar a shekarar 2006 da 2008, da ma shekarar 2019.
A shekarar 202 ƴan tawaye suka kashe tsohon shugaban ƙasar, Idriss Deby Itno, a bakin iyakar ƙasar da Libya da ke yankin arewaci.
A lokacin binne shi, shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron ya ce, “Faransa ba za taɓa bari zaman lumana ya samu tsaiko a Chadi ba."

Asalin hoton, AFP
Me zai iya biyo baya?
Chad ce ƙasa ta kwana-kwanan nan da ta bi sahun wasu ƙasashen a tsakiya da yammacin Afirka wajen yanke alaƙar soji da Faransa.
A ƴan shekarun da suka wuce, Mali da Nijar da Burkina Faso sun yanke alaƙa da Faransa da wasu ƙasashen na yamma, inda suka koma harkokinsu da Rasha domin neman gudunmuwarta.
Mai sharhi kan harkokin tsaro, Mr Abba ya yi amannar cewa matsalolin da Chadi za ta fuskanta kadan ne, saboda "ta riga ta nuna ƙwanjinta a ɓangaren soji."
Sai dai kuma yanke alaƙar ya zo a daidai lokacin da shugaban ƙasar Najeriya, Bola Tinubu ya ke ziyarar aiki a ƙasar Faransa.
Duk da Najeriya na cikin ƙasashen da Faransa ke alaƙa da su domin yaƙi da ta'addanci a yankin, wasu kafofin sadarwa a Faransa sun ce tattaunawar ziyarar ta mayar da hankali a kan harkokin tattalin arziki.
Har yanzu dai babu tabbaci ko ƙasashen biyu za su kafa sansanin sojin Faransa a Najeriya. Wani tsohon hafsan soji, Umar Aliyu, wanda ya yi ritaya a muƙamin kyaftin, wanda yanzu yake sharhi kan harkokin tsaro ya shaida wa BBC cewa, yana kokwanton kasancewar hakan.












