Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Madrid za ta sayi Alexander-Arnold, City za ta yi cefane a Janairu, Utd na son Xavi
Real Madrid ta shirya ɗaukar ɗan bayan Ingila Trent Alexander-Arnold, mai shekara 25, a lokacin da kwantiraginsa da Liverpool zai ƙare a bazara mai zuwa
to amma kuma wataƙila ta neme shi a watan Janairu yanzu bayan da ɗan bayanta na Sifaniya Dani Carvajal, mai shekara 32, ya ji mummunan rauni a gwiwarsa. (Sport)
Liverpool na ci gaba da tattaunawa a kan maganar kwantiragin manyan 'yan bayanta biyu -Jarell Quansah mai shekara 21 da kuma Ibrahima Konate, na Faransa mai shekara 25. (Mirror)
Paul Pogba, mai shekara 31,na tattaunawa da Juventus domin kawo ƙarshen zamansa na biyu a ƙungiyar, sannan kuma ya fara sabo bayan da kotun wasanni ta duniya ta rage tsawon hukuncin haramcin da ta yi masa. (Mail)
Wolves ba ta da niyyar korar kociyanta Gary O'Neil maimakon haka za ta ba shi lokaci ya daidaita al'amura bayan cinta da aka yi sau shida a wasan Premier bakwai da ta yi zuwa yanzu. (Telegraph)
Manchester City ta ware fam miliyan 80 da za ta yi cefanen 'yanwasa a watan Janairu bayan da Rodri ya ji raunin da zai yi jinya har zuwa ƙarshen kaka. (Football)
West Ham na sha'awar dawo da tsohon ɗan gaban Leicester da Newcastle Ayoze Perez, gasar Premier da nufin cewa ɗan wasan na Vuillareal mai shekara 31 zai ƙarfafa gaban ƙungiyar. (Caught Offside)
Ana ganin tsohon kociyan Barcelona Xavi a matsayin wanda ya fi dacewa wajen sake gina Manchester United idan Erik ten Hag ya bar Old Trafford. (El Nacional)
Shirin Newcastle United na sayen Jonathan David na Lille ya gamu da ciksa bayan da Barcelona ta fara cinikin ɗan gaban mai shekara 24. (Shields Gazette)
Liverpool ta bi sahun Newcastle da Tottenham wajen ƙokarin sayen ɗan wasan tsakiya na Crystal Palace Eberechi Eze mai shekara 26. (Football Insider)
Barcelona na sa ido a kan ɗan wasan gaba na gefe na Bayern Munich Leroy Sane, mai shekara 28, wanda kwantiraginsa zai ƙare a ƙarshen kaka. (Sport)
Ƙungiyoyin Premier da suka haɗa da Arsenal, da Wolves, da Everton da kuma Chelsea na sa ido a kan matashin ɗan bayan Santos Joao Pedro Chermont na Brazil mai shekara 18. (Caught Offside)