Slot ya zama na farko a Liverpool da ya ci wasa tara daga 10 da ya ja ragama

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kociyan Liverpool, Arne Slot ya zama na farko da ya ja ragamar wasa 10 da fara kaka, sannan ya ci karawa tara daga ciki.

Ranar Asabar Liverpool ta je ta yi nasarar cin Crystal Palace 1-0 a wasan mako na bakwai a Premier League da suka kara a Selhurst Park.

Tun a minti na tara da take leda, Liverpool ta ci ƙwallon ta hannun Diogo Jota, hakan ya sa ta haɗa maki ukun da take bukata.

Slot, tsohon kociyan Feyenoord ya maye gurbin Jurgen Kloop a Liverpool, bayan da aka kammala kakar da ta wuce, bayan kaka tara da ɗan Jamus ya yi a Anfield.

Kawo yanzu Liverpool tana matan farko a teburin Premier League da maki 18, wadda Nottingham Forest ce ta doke ta 1-0 a Anfield ranar 14 ga watan Satumba.

Bayan wasa bakwai da Liverpool ta yi da fara kakar nan, ta yi nasara shida aka doke ta wasa ɗaya, sannan ta ci ƙwallo 13 aka zura mata biyu a raga da rara 11 kenan.

Haka kuma a gasar Champions League ta kakar nan, Slot ya je ya doke AC Milan 3-1 ranar 17 ga watan Satumba da kuma cin Bologna 2-0 ranar 2 ga waan Oktoba a Anfield.

Wasa uku da ke gaban Liverpool:

English Premier Lahadi 20 ga watan Oktoba 2024

  • Liverpool da Chelsea

Champions League Laraba 23 ga watan Oktoba 2024

  • RB Leipzig da Liverpool

English Premier Lahadi 27 ga watan Oktoba 2024

  • Arsenal da Liverpool