Champions League: Arsenal ta yi canjaras, Monaco ta doke Barcelona

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal ta fara gasar champions league ta bana da canjaras inda wasanta da Atalanta ya ƙare 0-0, a filin wasan Gewiss da ke yankin Bergamo a ƙasar Italiya.

Golan Arsenal David Raya ya tare fenariti a minti na 51 domin ya tabbatar da cewa ƙungiyarsa ba ta yi rashin nasara a wasanta na farko a gasar ba.

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya yi magana kafin wasan inda ya bayyana fatan cewa ƙungiyar za ta yi nisa a gasar bana.

Da wannan sabon tsarin gasar na bana zai yi wahala a iya gane ko sakamakon zai yi tasiri a yunƙurin da ƙungiyar ke yi na taɓuka abin kirki a bana, amma Atalanta - wadda ta lashe gasar Europa League a bara - ba kanwar lasa ba ce don haka ana iya ganin samun maki guda a filin wasansu a matsayin kyakkyawar sakamako.

Yanzu Arsenal za ta karkata akalarta zuwa wasanta na gaba a gasar Premier inda za ta kece raini da Manchester City a ƙarshen wannan makon.

A ɗaya daga cikin wasannin da aka fafata kuma Barcelona ta fara gasar bana da rashin sa'a inda ta sha kashi a hannun Monaco da ci 2-1.

Ɗan wasan Najeriya George Ilenikhena ne ya zura ƙwallo a wasansa na farko a gasar wanda hakan ya taimakawa Monaco yin nasara kan Barcelona wanda ta ƙare wasan da ƴan wasa 10 a fili bayan an danna wa Eric Garcia jan kati a minti na10 da fara wasa.

Monaco ce ta fara zura ƙwallo a raga ta hannun Maghnes Akliouche a minti na 16 kafin Lamine Yamal ya farkewa Barcelona a minti na 28.

Ilenikhena mai shekara 18 ne ya ƙarasa ƙungiyar Hansi Flick inda ya zura ƙwallo a minti na 71.

Wasan Barcelona na gaba zai zo ne a gasar La Liga inda za ta nufi gidan Villareal ranar lahadi 22 ga watan satumba.

Yadda sauran wasanni suka kasance

An ci jimillar ƙwallaye 16 a dukkan wasannin da aka buga a ranar Alhamis:

Fayenoord 0 Bayer Lverkusen 4

Crevena Zvezda 1 Benfica 2

Brest 2 Sturm Graz 1

Atletico Madrid 2 RB leipzig 1

Za a ci gaba da fafatawa a gasar ta bana a ranar Talata daya ga watan Oktoba.