Barazanar ƙarin harajin Trump ta gigita kamfanonin Amurka

- Marubuci, Natalie Sherman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Lokacin da mai zanen jakar hannu Sherrill Mosee ta sami labarin cewa kusan jakunkunan hannu 2,700 da jakunkunan ratayawa da ta yi oda daga wani kamfani da take hulda da shi a China, ba za su shiga jirgi ɗaya ba a wannan kaka, da farko abin bai dame ta ba.
Daga baya kuma aka sake zaɓar Donald Trump a matsayin shugaban ƙasar Amurka.
Ms Mosee, wadda ta kafa MinkeeBlue, wata ƙaramar masana'anta a Philadelphia ta ce "Ina son dole mu shigo da waɗannan." Kamfanin nata na ɗaya daga cikin dubbai a faɗin ƙasar da ke shirya wa ganin tasirin alƙawurran da Trump ya yi na sanya wasu tsauraran haraji kan duk kayayyakin da ke shigowa ƙasar.
Barazanar ta ɗauki hankali a wannan mako, yayin da Trump ya ce zai ɗauki matakai a ranarsa ta farko bayan rantsar da shi.
Ya ɗauki aniyar ɗaukar matakai - ciki har da ɓullo da harajin kan iyaka - kan kayayyakin China da Mexico da kuma Canada, manyan abokan hulɗar kasuwancin Amurka uku.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Donald Trump ya ce yana shirin ƙaƙaba harajin kashi 25 cikin 100 kan kayayyakin Canada da Mexico da kuma ''ƙarin harajin kashi 10, kan hakan ga kayyakin ƙasar China.
Wannan saƙo da ya wallafa na zuwa ne bayan alƙawarin da ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓe na ƙaƙaba harajin kayayyakin da ke shiga Amurka da aƙalla kashi 10, da kuma ƙarin kashi 60 ko fiye kan kayyakin ƙasar China - waɗanda da dama ke fuskantar biyan bashin haraji da aka ƙaƙaba musu a lokacin wa'adin mulkinsa na farko.
Wasu masana sun ce manufofin Trump na iya kasancewa marasa tasiri fiye da alƙawarin, kuma ya kamata a fahimci kalaman nasa a matsayin somin-taɓi a manyan alƙawuran da ya ɗauka da suka shafi baƙin haure da miyagun ƙwayoyi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ba tare da la'akari da yadda manufofin ke tasiri ba, barazanar ta samu karɓuwa, yayin da kamfanoni kamar MinkeeBlue suka fara tunanin canja hanyar safarar kayayyaki da sake fasalin kwangila da ɗaukar wasu matakai don kiyaye tasirin hakan.
Chris Caton, manajan darakta a cibiyar dabaru da nazari a babban kantin sayar da kayayyaki na Prologis, ya ce kamfaninsa ya ga tashin hankali a cikin ayyukan "a gefe" yayin da 'yan kasuwa ke fargabar samun ƙarin haraji bayan da suka fara neman mafita.
''Akwai tasiri kan tattalin arziki, ko dai na bunƙasa ko na faɗuwa'', in ji Wendy Edelberg, daraktan cibiyar tattalin arziki ta Hamilton.
A kwanakin bayan zaɓen, babban kamfanin sayar da takalma Steve Madden ya shaida wa masu zuba jari cewa, yana ci gaba da shirin canza masana'antu a wajen ƙasar China, da nufin rage shigo da kayayyaki daga ƙasar cikin rabin shekara mai zuwa.
Kamfanin ƙera kayan aiki da kayan masarufi na Stanley Black & Decker ya ce ya fara tattaunawa da abokan cinikinsa game da hauhawar farashin da aka danganta da ƙarin haraji.
Haka suma shugabannin kamfanin Walmart na tattana makamancin wannan shiri.
Ko da manufofin Trump sun ci gaba da wanzuwa, Ms Edelberg ta ce jama'a na iya ganin ƙaruwar farashi, da kuma ƙarancin wasu kayayyaki, yayin da ajiye kayyaki ya bar wasu kamfanoni cikin ruɗani.
''Kamar yadda wasu kamfanoni ba su da tabbas game da abin da zai faru, shi ma hakan zai iya kawo cikas ga ci gaban tattalin arziki a cikin watanni masu zuwa'', in ji ta.

Asalin hoton, Getty Images
Trump da masu ba shi shawara sun ce ƙarin harajin zai taimaka wajen farfaɗo da kamfanonin Amurka tare da bunƙasar ƙarin ayyukan yi.
To sai dai masana tattalin arziki sun ce hakan zai faru ne a lokacin da wasu kamfanonin za su yi asara.
Martin Pochtaruk, shugaban kamfanin haɗa sola na ƙasar Canada, Heliene, ya ce a shekarar 2018 sai da kamfaninsa ya kusan rufe ayyukansu sakamakon ƙarin haraje-haraje da Tarump ya ɗora wa kamfanonin sola na ƙasashen waje a wa'adin mulkinsa na farko.
A yanzu kuma kamfanin ne ƙera duka kayayyakinsa a Amurka, inda ya ɗauki mutum 400.
Da dama daga cikin masu sari a kamfanin sun kakkafa shaguna a Amurka, sakamakon ƙarfafa su da gwamnatin ƙasar ta yi ƙarƙashin shirin sabunta makamashi da Shugaba Biden ya ɓullo da shi.
Kamfanin Mista Pochtaruk ya koyi darasi a baya, lamarin da ya sa ya sauya tsarin kwantiraginsa, domin kwastomominsa su san irin sauye-sauyen da za a samu kan haraji, kamar yadda ya faru lokacin annobar covid.
Sai dai duk da wannan kariyar, yiwuwar sake sabunta taƙaddamar kasuwanci tsakanin ƙasashe masu kyakkyawar alaƙa kamar yadda Canada da Amurka na ƙara haifar da damuwa, in ji Mista Pochtaruk.

Asalin hoton, Getty Images
Masana tattalin arziki sun ce harajin da ake amfani da shi gomman shekaru a kamfanonin samar da tufafi da takalma ya nuna cewa za su iya kare wasu kamfanoni, tare da fatan haɓaka ayyukan yi, yayin da suka ƙara farashin kayyakin da da suke sarrafawa.
Hukumar Kula da Kasuwanci ta Amurka (NRF) ta yi gargaɗin cewa ƙarin haraji da kuma amfani da shawarwarin yaƙin neman zaɓen Trump zai jawo wa kamfanonin asarar kuɗin da suka kai dala biliyan 46 da ƙarin dala biliyan 78 a duk shekara ga kamfanonin samar da tufafi da kayan wasa da kayan ɗaki da kayyakin amfanin gida da takalma da kayayyakin tafiye-tafiye.
A ranar Litinin matakin Trump kan Mexico - wadda ta fi shigar da lemuka da kayan marmari Amurka, ƙarƙashin yarjejeniya kasuwanci maras shinge da ta jima tsakaninsu - ya haifar da ce-ce-ku-ce musamman kan alƙawarin ƙarin haraji da sauran alƙawura na rage farashin kayyaki ga Amurkawa.

Yayin da ƙananan kamfanoni ke fuskantar ƙaruwar gasa tsakaninsu, Ms Mosee ta ce ba ta tunanin ƙara farashin jakankunan da kamfaninta ke haɗawa, wadda ta ke sayarwa kan dala 180 kowace guda.
A yanzu tana tunanin faɗaɗa kasuwancinta ta hanyar neman abokan ciniki daga ƙasashe irin su Cambodiya da Indiya.
Bayan shekara goma da fara kasuwancin nata, Ms Mosee - wadda tsohuwar injiniya ce - ta ce mai yiwuwa tana buƙatar samun sabbin abokan kasuwanci idan har ƙaramar masana'antar tata mai ma'aikata biyu, ta iya ci gaba da wanzuwa bayan sauye-sauyen harajin da ake sa ran faruwarsu bayan rantsar da Trump a karo na biyu.
"Abu ne mai wahala," in ji ta. "Zai yi matuƙar wahala sosai kuwa''.










