Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Anthony Blinken zai kai ziyara Gabas ta Tsakiya?
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai kai ziyara Isra'ila a wani yunƙuri na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma sako waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza.
Tun da farko, ofishin firaiministan Isra'ila ya ce akwai abubuwan da zasu amince da su dake ƙunshe cikin sabuwar yarjejeniyar da Amurka ta gabatar..
Wakilin BBC ya ce ƙarƙashin wannan yarjejeniyar akwai batun tsagaita wuta da kuam sako wadanda aka yi garkuwa da su a Gaza da kuma Falasdinawa dake gidan yarin Isra'ila.
Sai dai kafar watsa labaran isra'ila ta ruwaito cewa ba a saka muhimman sharuddan da Isra'ila ta gabatar ba, wadanda suka hada da ci gaba da jibge sojojinta kan iyakar Gaza da Masar, wanda Hamas ta ce ba ta amince da shi ba tun farko.
Hamas ta ce duk wani shirin tsagaita wuta a Gaza zai dogara ne kan tattaunawar da aka yi tun a watan Yuli, wato wata ɗaya da rabi da ya gabata kenan, maimakon fara sabon zagaye na shawarwari.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadin da ta gabata, ƙungiyar ta buƙaci masu shiga tsakani "su gabatar da wani shiri na aiwatar da abin da kungiyar ta amince da shi a ranar 2 ga Yulin 2024, bisa manufar Shugaban Amurka Joe Biden da kuma ƙudirin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya".
A ranar 2 ga watan Yuli Hamas ta mayar da martani ga shawarar tsagaita buɗe wuta da Shugaba Biden ya gabatar a ranar 30 ga watan Mayu.
Yayin da ba a bayyana cikakken martanin Hamas a filli ba, an fahimci cewa kungiyar ta nemi a kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya a farkon kwanakin yarjejeniyar maimakon a tsakiyar yarjejeniyar kamar yadda Biden ya gabatar.
An kuma ci gaba da tattaunawar mako guda bayan martanin Hamas, amma tattaunawar ta yi tsami saboda sabbin sharuɗɗaan da Isra'ila ta gabatar.