Al-Hilal ta shata wa Fernandes wa'adi, Ronaldo zai bar Saudiyya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya ta gabatar da tayinta kan Kyeftin ɗin Manchester United, Bruno Fernandes na Portugal mai shekara 30, sannan ta faɗa ma sa yana da wa'adin sa'o'i 72 ya yanke hukunci kan amincewa da yarjejniyar ko akasin haka. (Mail, external)

Manchester City ta bi sahun masu fafutukar ɗan wasan Lyon mai shekara 21 daga Faransa, Ratan Cherki da ke buga tsakiya. Ana dai alakanta ɗan wasan da Liverpool da Chelsea. (Telegraph - subscription required, external)

Everton ta bi sahun Leeds United a farautar ɗan wasan nan mai shekara 33 daga Newcastle United da Ingila, Callum Wilson, wanda ba shi da kwantiragi a hannu. (The Sun, external)

Tottenham ta bada kofar iya sayen ɗan wasan Bayern Munich da Jamus, Leroy Sane mai shekara 29, wanda kwantiraginsa ke karewa a watan gobe.(Sky Sports, external)

Aston Villa na son daidaitawa da ɗan wasan Feyenoord, mai shekara 18, Zepiqueno Redmond a sabuwar kaka. (Sky Sports, external)

Arsenal ta tattauna da wakilin ɗan wasan Sporting, Viktor Gyokeres a Lisbon tare da gabatar da tayin fam miliyan 58.7 ga ɗan wasan na Sweden. (Correio da Manha - in Portuguese, external)

Manchester United ta amince da sharudan cimma yarjejeniya da ɗan wasan Ipswich, Liam Delap inda take jiran hukunci daga ɗan wasan na gaba. (ESPN, external)

Ɗan wasan Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara 40, na shirin barin ƙungiyarsa ta Al-Nassr da ke Saudiyya, domin cimma sabuwar kwantiragi da wata ƙungiyar gabanin soma wasannin ƙungiyoyin duniya da za a soma a ranar 15 ga watan Yuni a Amurka.(Telegraph - subscription required, external)