Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa majalisa ke son a yi zaɓen shugaban ƙasa a 2026?
Majalisar dokokin Najeriya tana shirin yi wa dokar zaɓen ƙasar 2022 gyaran fuska ta yadda za a iya gabatar da zabukan shugaban ƙasa da na gwamnoni watanni shida gabanin ƙarewar wa'adinsu.
Idan har daftarin ƙudirin ya samu amincewar ƴan majalisar tare da samun sa-hannun shugaban ƙasa ya zama doka, za a gudanar da babban zaɓen ƙasar a watan Nuwamban 2026 maimakon watannin Fabrairu da Maris na 2027.
Daftarin wanda ɗaya ne a cikin jerin jadawalin gyare-gyaren fuska da za a yi wa dokar zaɓen ta 2022, ya ce "dole zaɓukan shugaban ƙasa da na gwamnoni a kammala su aƙalla kwana 185 kafin ƙarewar wa'adin shugabanni masu ci."
A yanzu haka dai daftarin mai suna Ƙudirin dokokin zaɓe na 2025 na matakin sauraron ra'ayoyin jama'a da kwamitin haɗaka na majalisar dokokin ƙasar dangane da batutuwan da suka jiɓanci zaɓe.
Kuma ana sa ran mahalarta tarukan jin ra'ayoyin jama'ar ka iya ƙara wasu abubuwan da suke ganin ya kamata ya shiga cikin dokar zaɓe ta ƙasar gabanin zaɓen 2027.
Dalilin sauya lokacin zaɓen shugabanni
Ƴanmajalisar sun ce manufar sauya lokacin zaɓukan shi ne tabbatar da kammala duka shari'o'in ƙorafe-ƙorafen zaɓe kafin ranar 29 ga watan Mayun 2027, ranar da za a rantsar da shugaban ƙasa da gwamnoni.
"A da sai da ka ci zaɓe kawai za a rantsar da kai sai kuma a je a yi ta fitina a kotu. To yanzu so ake a bai wa masu shari'a damar duka kammala shari'u kafin a rantsar da waɗanda suka ci zaɓe, Kenan idan ana son yin hakan dole ne a yi zaɓe da wuri," in ji Sanata Yahya Abdullahi, ɗan majalisar dattawa da ke wakiltar jihar Kebbi.
Illa ko amfanin sauya lokacin zaɓen shugaban ƙasa
Malam Kabiru Sufi masanin kimiyyar siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a Kano, CAS, ya ce al'amarin na da fuska guda biyu.
"Fuskata ɗaya shi ne akwai tunanin akwai siyasa a wajen bujuro da shi wato tun siyasa da ƙarfinta sannan shugabannin ma da ƙarfinsu za su iya yin abin da za su yi wajen samun nasara a lokutan zaɓensu. Saboda haka ana ganin idan aka bar shi kamar yadda yake wato wata uku kafin ƙarewar wa'adinsu da wuya su iya yin tasiri."
"Wasu kuma suna duban sa cewa abu ne mai kyau cewa idan an yi zaɓe gwamnatin da za ta shiga tana da damar shiryawa da sauransu. To sai dai ko da da wannan fuskar aka duba idan har an samu sauyi to shi kuma wanda ya kasance zai sauka ɗin to ba zai iya yin komai ba a ragowar lokacin da ya rage masa. Abin da ya sa wasu ke ganin ya kamata a bar dokar lokutan zaɓen a yadda suke."
Sauya lokacin zaɓe a 2015
A shekarar 2015 ne hukumar zaɓen Najeriya ta sanar da sauya lokacin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa daga watan Fabrairu zuwa Maris.
"An akaƙanta dalilin yin hakan da wata sara da magoya bayan Muhammadu Buhari suka tsira a lokacin ta "FeBuhari" wadda ba ta yi wa jam'iyya mai mulki daɗi ba. Hakan ne ya sa aka ɗage lokacin zuwa watan Maris.
"Har wayau dai magoya bayan Buharin suka mayar da saran tasu zuwa "March For Buhari". In ji Malam Kabiru Sufi.
Sauran abubuwan da daftarin ya ƙunsa
- Sauya lokacin zaɓen majalisar dokoki da ta jihohi inda za a rinƙa gudanar da zaɓukan kwanaki 185 kafin ƙarshen wa'adinsu.
- Ƴancin fursunoni na yin rijista da kaɗa ƙuri'a
- Samar da hanyar tantance masu zaɓe ta intanet
- Ɗaukar tsauraran matakai kan laifukan zaɓe da suka haɗa da zaman gidan kaso na dole ga fitar da sakamakon zaɓe na ƙarya ko kuma hana jami'an zaɓe gudanar da ayyukansu.
- Gyara tsarin wakilai masu zaɓe da ake kira da 'delegate'
- Gudanar da bincike kan kashe kuɗaɗen INEC a watanni shida a kowace shekara
- Ƙayyade yawan kuɗaɗen kamfe domin dacewa da yanayin tattalin arziƙin da ƙasa ke ciki.
- Zaɓen wuri ga ƴan Najeriyar da ayyukansu ba za su bar su su kaɗa ƙuri'a ranar zaɓe ba
- Bai wa INEC damar sake waiwayar sakamakon zaɓen da aka ayyana ta hanyar matsin lamba ko kuma aka tilasta malamin zaɓe ayyanawa.