Leicester City ta kori kociyanta Cooper

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Leicester City ta kori, Steve Cooper, bayan da take ta 16 a teburin Premier League daga karawa 12.

Ƙungiyar ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Chelsea a gida karkashin tsohon kociyanta, Enzo Maresca ranar Asabar.

Rashin nasarar da Leicester City ta yi, ya sa tana da tazarar maki biyu tsakaninta da ƴan ukun karshe a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Cooper ya karɓi aikin daga Maresca, bayan da ya kai Leicester gasar Premier daga Championship kan fara kakar nan.

Tuni ƙungiyar ta sanar da naɗa Ben Dawson a matakin riƙon ƙwarya, yayin da Danny Alcock da kuma Andy Hughes za su taimaka masa.

Mataimakin Cooper, Alan Tate da Steve Rands duk sun bar ƙungiyar.

Bayan rashin nasara da Leicester ta yi a kan Chelsea, karo na shida da aka doke ta kenan a kakar nan, kuma Cooper ya caccaki alkalin wasa, Andrew Madley kan yadda ya busa karawar ta ranar Asabar.

Shi ne kociya na biyu da ya rasa aikinsa a Premier League, bayan da aka raba gari tsakanin Manchester United da Erik ten Hag cikin watan Oktoba.

Cooper ya karɓi jan ragamar Leicester City, bayan aiki da ya yi da Nottingham Forest, wadda ta kore shi cikin Disambar 2023.

Mai shekara 44 shi ne ya kai Leicester gasar Premier League a 2022 daga baya aka kore shi a kakar 2023/24 lokacin da ƙungiyar ke mataki na 17 a teburi.

Haka kuma Cooper, wanda ya ja ragamar tawagar matasan Ingila ƴan shekara 17 da ta lashe kofin duniya a 2017 ya horar da Swansea City a baya.