Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ke kunshe cikin bayanan binciken mutuwar Jeffrey Epstein
- Marubuci, Shayan Sardarizadeh
- Marubuci, Matt Murphy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Gargadi: wannan labari na dauke da bayanan da za su iya tayar da hankalin mai karatu
Gwamnatin Amurka ta fitar da wasu hotunan gawar jeffrey Epstein wanda ba a gani ba a baya, da ke nuna likitoci a kansa jim kadan bayan mutuwarsa.
Hotunan guda 20 wadanda yawanci ba su da kyawun gani, an wallafa su ne a wani bangare na rahoton binciken gawar Epstein da hukumar FBI ta yi, da abin da ya janyo mutuwarsa da kuma wasu takardu na gidan yari.
Suna cikin miliyoyin takardu da ma'aikatar shari'a ta Amurka ta wallafa ranar Juma'a, a cikin wani bangare na badaƙalolin Epstein.
Epstein ya mutu a wani gidan yari na birnin New York ranar 10 ga watan Agustan 2019 yayin jiran shari'a.
An tsare shi ne kan zargin safarar mutane domin aikata lalata.
Sabon rahoton na hukumar FBI mai taken "binciken mutuwar Jeffrey Epstein", ya nuna yadda ofishin hukumar a New York ke bincike kan dalilin mutuwarsa. Rahoton mai shafi 23 yana dauke da hatimi da aka buga a kowane shafi.
Takardun wadanda ke dauke da cikakkun bayanai wanda BBC ta gani, sun nuna hoton wuyar Epstein da kuma wasu raunuka. Suna kuma dauke da bayanai na binciken mutuwarsa da wani rahoto kan lafiyar kwakwalwarsa, kwanaki kafin ya kashe kansa.
Hotuna da dama sun nuna Epstein kwance kan karamin gadon daukar marasa lafiya yayin da likitoci ke kokarin farfado da shi. Hotunan na dauke da kwanan wata ranar 10 ga Agustan 2019 wanda aka dauka da misalin karfe 6, mintuna 16 bayan samun baya motsi a dakinsa na gidan yari.
Ba a san ainihin wurin hoton ba, sai dai an garzaya da Epstein zuwa wani asibiti da ke kusa da misalin karfe 06:39 inda aka sanar da cewa ya mutu, abin da ke nufin cewa a can aka dauki hotunan.
Wasu karin hotuna guda uku na dauke da alamomi da ke nuna cewa an dauke su a asibitin. Sun nuna kansa da kuma wani rauni a wuyansa. An rubuta sunan Epstein a kan kowane hoto, sai dai ba a rubuta farkon sunansa da kyau ba "Jeffery" maimakon Jeffrey a wasu hotunan.
Sashen tantance bayanai na BBC ya gudanar da bincike kan sabbin hotunan gawar Epstein da aka fitar, kuma bai ga inda aka taba wallafa irin hotunan ba kafin ranar 30 ga watan Janairu.
Mun kuma samu takardu cikin wadanda aka fitar da suka yi kama da wasu, ciki har da rahoton binciken mutuwar Epstein mai shafi 89 da ma'aikatar shari'a ta Amurka da kuma ofishin babban mai bincike kan lafiya a New York suka fitar, har ma da sakonnin email daga ofishin FBI a New York.
Wani bangare na binciken rahoton mutuwar Epstein ya bayyana a gaban kotu, ciki har da gwaje-gwaje biyu na raunuka da ke wuyansa.
Rahoton ya kuma kunshi bayanai na lokacin da aka tsare Epstein a gidan yarin New York, bayan kama shi kan laifin safarar mutane don yin lalata ranar 6 ga watan Yulin 2019 har zuwa mutuwarsa.
Har ila yau, rahoton ya bayyana cewa an saka ido kan Epstein bayan da aka ga yana son kashe kansa ranar 23 ga Yulin 2019.
Ya zargi abokin zamansa a gidan yarin - Nicolas Tartaglione, wani tsohon jami'in dansanda da ke fuskantar tuhuma kan kisa - da yunkurin kashe shi a lokacin.
A wani zama da masanin halayyar dan'adam washegari, Epstein ya ce "ba ni da niyyar kashe kaina" kuma zai zama "abu mara kyau" ya dauki ransa, kamar yadda rahoton ya bayyana.
Ya bayyana ranar 25 ga Yuli cewa "ba zan iya daukar raina ba, kuma ina son komawa yin rayuwata", a cewar rahoton masanin halayyar dan'adam din.
Wasu bayanai da ma'aiktar shari'a ta Amurkan ta fitar sun nuna cewa jami'in gidan yarin ya ba da shawarar cewa kada a bar Epstein a daki shi kadai kuma ya ce "a rika duba shi kowane bayan minti 30".
An sake abokin zaman Epstein a gidan yarin kwana guda kafin mutuwarsa. A daren 9 ga Agusta jami'in kula da fursunonin ya kasa zuwa yin dubiya wanda aka tsara yi da misalin karfe 3:00 da kuma 05:00, kamar yadda bayanan gidan yarin suka nuna, kuma na'urar daukar hoto na a sashen dakunan ba ya aiki.
An gano gawarsa washegari lokacin da jami'an gidan yarin ke zagayawa.
An kuma wallafa wani bangare na rahoton FBI wanda aka cire wasu muhimman bayanai mai shafi 17, a matsayin bangare na badakalolin Epstein.
Rahoton bai kunshi rahoton masanin halayyar dan'adam ba ko kuma lokacin da aka tsare Epstein, an kuma cire wasu hotuna. Ba a dai san me ya sa aka wallafa duka bayanan ba.
An tuntubi ma'aikatar shari'a ta Amurka don jin martani. Hukumar FBI ta ki cewa uffan.