Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Newcastle da Liverpool za su sake zama kan Isak, Man U na son sayar da Hojlund
Newcastle za ta sake tattaunawa da Liverpool wadda ke yukurin daukar ɗan wasanta na gaba kuma ɗan kasar Sweden Alexander Isak mai shekara 25 kan kudi fan miliyan 120 zuwa 130 .(Teamtalk), external
Wolves na kokarin ganin cewa ɗan was mai kai hari ɗan kasar Norway Jorgen Strand Larsen bai bar kungiyar ba yayin da Newcastle ta kara kaimi don siyansa kan fan miliyan 60. (Express and Star), external
Manchester United ta sanar da Napoli cewa a shirye take ta ba ta lamuni tare da zabi ko wajibcin siyan ɗan wasanta ɗa=an kasar Denmark Rasmus Hojlund, mai shekara 22. (Fabrizio Romano), external
Everton na son ta dauko ɗan wasa bayan Manchester City da Netherlands Nathan Ake mai shekara 30, domin karfafa 'yan wasan bayan kungiyar. (Mail), external
Manchester United na fatan Tottenham za ta shiga jerin kungiyoyin kwallon kafa da ke sha'awar ɗan mai kai hari ɗan kasar Argentina Alejandro Garnacho mai shekara 21, domin su fafata da Chelsea. (Givemesport), external
Fatan Roma na siyan ɗan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 25, daga Manchester United na iya dogara ne kan ko wakilinsa zai rage kudin Yuro miliyan 10 da ya nema a matsayin kwamisho kafin su kulla yarjejeniya(Corriere della Sport in Italian), external
Real Betis na fatan siyan ɗan wasa mai kai hari na Manchester United da Brazil Antony,mai shekara 25, sai dai ta nemi kungiyarsa ta yanke shawara kan makomarsa . (Mail), external
Tottenham na zawarcin ɗan wasan tsakiya na Faransa Maghnes Akliouche, mai shekara 23, da ke taka leda a Monaco da kuma dan wasan Como da Argentina Nico Paz mai shekara 20. (Telegraph - subscription required), external
Spurs na duba yiwuwar siyan dan wasan gaban Faransa Christopher Nkunku, mai shekara 27, daga Chelsea. (Teamtalk), external
Nottingham Forest ta tuntubi Aston Villa kan dawo da ɗan wasan bayan Poland Matty Cash, mai shekara 28, cikin kungiyar kuma sun yi wa Sevilla tayin siyan dan wasan bayanta,Jose Angel Carmona mai shekara 23. (Mail), external
West Ham ta amince ta bada aron ɗan wasanta kuma ɗan kasar Mexico Edson Alvarez mai shekara 27, ga Fenerbahce kuma suna zawarcin Werder Bremen da dan wasan tsakiya na kasar Austria Romano Schmid, mai shekara 25, kuma suna son dan wasan tsakiya na Lens kuma dan kasar Faransa French Andy Diouf mai shekara 22. (Guardian), external
Sai dai, Inter Milan na da kwarin gwiwa cewa za ta kulla yarjejeniya shekara biyar da Diouf kan kudi kusan yuro miliyan 25 (La Gazzetta dello Sport in Italian), external
Crystal Palace na kokarin ganin ta yi wa Everton pintikau a rige-rigen siyan ɗan wasan Southampton Tyler Dibling mai shekara 19, ta hanyar yi masa tayin fam miliyan 35 . (Givemesport), external
Borussia Dortmund na sa ran kamala cinikin siyan ɗan wasan gaban Wolves da Portugal Fabio Silva, mai shekara 23, (Bild in German), external