Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal na harin Gibbs-White, Al-Hilal na zawarcin Raphinha
Arsenal na sa ido a kan dan wasan tsakiya na Nottingham Forest Morgan Gibbs-White, dan Ingila domin kungiyar ka iya sayar da shi domin ta daidaita lalitarta. (Star)
Shugaban Barcelona Joan Laporta ya ce kungiyar ta yi watsi da tayin da aka yi mata na yuro miliyan 200 a kan matashin danwasan gaba na Sifaniya Lamine Yamal. (Marca)
Kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya na son sayen dan wasan gaba na gefe na Brazil Raphinha daga Barcelona, kuma a shirye take ta bayar da kudin da ya kai yuro miliyan 100 a kansa (Sport )
Newcastle United na son sayen dan bayan Portugal Goncalo Inacio, mai shekara 22, da kuma dan bayan Ivory Coast Ousmane Diomande, mai shekara 20, daga Sporting Lisbon amma kuma dokokin kashe kudi ka iya hanasu. (Fichajes )
Kylian Mbappe ba zai sanar da tafiyarsa daga Paris St-Germain zuwa Real Madrid ba, saboda yuwuwar haduwar kungiyoyin biyu a gasar Zakarun Turai (Champions League). (Sport )
Juventus na duba yuwuwar sayen Mason Greenwood, wanda ke zaman aro a Getafe daga Manchester United, inda kwantiraginsa a Old Trafford zai kare a 2025. (Gazzetta dello Sport )
Ba lalle ba ne Eintracht Frankfurt ta nemi sayen dan wasan tsakiya Donny van de Beek na Holland da ke zaman aro a kungiyar, daga Manchester United domin ya zauna dindindin. (Bild daga Goal)
Kociyan Manchester United Erik ten Hag yana ganin har yanzu yana da damar shawo kan, daya daga cikin masu kungiyar, Sir Jim Ratcliffe domin barinsa ya ci gaba duk da cewa an yi maganar wanda zai maye gurbinsa. (ESPN)
Manchester United ba za ta nemi sayen Sofyan Amrabat da ta karba aro daga Fiorentina, ba. Kungiyar Ac Milan da kuma Juventus na son dan gaban na Moroko.(Tuttosport daga Football Italia)
Babban dan bayan Juventus Gleison Bremer, shi ne na farko da Manchester United ke son saye a bazara. Kuma dan wasan na Brazil na da yarjejeniyar sayar da shi a kan yuro miliyan 50. (Corriere dello Sport )
Napoli ba ta da niyyar sayen dan wasan tsakiya na Belgium Leander Dendoncker, wanda a yanzu yake zaman aro a kungiyar ta Italiya daga Aston Villa.(Fabrizio Romano)
Barcelona na son rike matashin dan bayan Pau Cubarsi, mai shekara 17, ta hanyar kulla sabon kwantiragi da shi bayan da kungiyoyin Premier suka fara nuna sha'awarsa. (Marca)