Saka ya fita daga cikin tawagar Ingila

An wallafa

Bukayo Saka ya janye daga cikin tawagar Ingila da za ta buga wasan sada zumunci tsakaninta Brazil da Belgium saboda rauni.

Dan wasan Arsenal mai shekaru 22, bai shiga cikin horo ba tun da aka kira cikin ƴan wasan kasarsa.

Hukumar ƙwallon Ingila ta ce Saka ya shiga sansanin 'yan wasan a St George's Park dauke da rauni.

Ingila za ta fafata da Brazil a Wembley a ranar Asabar kafin ta karɓi baƙuncin Belgium a ranar 26 ga watan Maris.

Janyewar Saka babbar koma baya ce ga kocin Ingila Gareth Southgate.

Ingila za ta buga ƙarin wasannin sada zumunci a ranakun 3 da kuma 7 ga watan Yuni, inda za ta kara da Bosnia-Herzegovina da kuma Iceland kafin soma gasar kwallon Turai mai laƙabin Euro 2024.