Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fulham ta kammala daukar Andreas Pereira daga Man United
Fulham ta kammala daukar dan kwallon Brazil, Andreas Pereira daga Manchester United.
Kungiyar da ke birnin Landan ba ta fayyace kan nawa ta dauki dan kwallon ba, amma an fahimci cewar cinikin ya kai fam miliyan 10 har da karin tsarabe-tsarabe.
Mai shekara 26 ya saka hannu kan kwantiragin kaka hudu tare da kungiyar da Marco Silva ke jan ragama, wadda za ta buga Premier League a kakar nan, bayan da ta lashe Championship a kakar da ta wuce.
Ya koma United a 2012, sai dai ya kasa samun gurbin buga wasanni sosai, inda aka bayar da shi aro ga Granada da Valencia da kuma Lazio.
Pereira ya yi wsa 74 a kungiyar Manchester United da cin kwallo hudu.Pereira zai zama na biyu da Fulham ta dauka a bana, bayan Joao Palhinha daga Sporting Lisborn da aka saya kan fam miliyan 17.
Fulham za ta buga Premier League a bana, bayan da ta fafata a Champions League a kakar da ta wuce.