Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta ci gaba da jan ragamar teburin Premier
Arsenal ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin Premier League, bayan da ta doke abokiyar hamayya Tottenham a Emirates ranar Asabar.
Gunners ta yi nasara da ci 3-1, inda Thomas Partey ya fara ci mata kwallo, Harry Kane ya farke a bugun fenariti.
Karo na bakwai da ya ci Arsenal kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron raga, sannan na 100 da ya zura a raga a wasannin waje a Premieer League.
Daga baya Arsenal ta kara biyu ta hannun Gabriel Jesus da kuma Granit Xhaka.
Tottenham ta karasa karawar da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Emerson jan kati.
Haka kuma karo na biyar da aka bai wa dam wasan Tottenham jan kati a lokacin fafatawa a gidan Arsenal a wasan na hamayya na Arewacin Landan.
Da wannan sakamakon Arsenal ta hada maki 21 da cin karawa bakwai da rashin nasara daya a hannun Manchester United.
Wannan shi ne karon farko da Tottenham ta yi rashin nasara a bana a babbar gasar tamaula ta Ingila, bayan cin wasa biyar da canjaras biyu.
Arsenal za ta buga Europa League da Bodo nan gaba, ita kuwa kuwa Tottenham za ta kece raini da Frankfurt.