World Cup 2022: An yi waje da Jamus, Japan da Sfaniya sun tsallake

.
An wallafa

Jamus ta fice daga gasar cin kofin duniya duk da nasara da ta yi 4-2 a wasanta da Costa Rica.

Ta kammala wasanninta ne da maki hudu, kuma tana jiran Sfaniya ta doke ko ta yi kunnen doki da Japan amma hakan ba ta samu ba.

A maimakon haka Japan ta doke Sfaniya ne 2-1, wanda haka ya bata damar mamaye rukunin na E da maki shida, yayin da Sfaniya ke binta da maki hudu, kuma ta hau kan Jamus ne da tazarar kwallaye biyar.

Ko a shekarar 2018 Jamus ba ta iya kaiwa zagayen kwaf daya ba, kuma sai gashi ko yanzu tarihi ya maimaita kansa.

A yanzu Japan za ta kwashi yan kallo da Croatia ranar Litinin, yayin da Sfaniya za ta hadu da Morocco ranar Talata.

Costa Rica ce ta zo ta karshe a rukunin da maki uku.