Amfanin da ƙwaƙwalwa ke samu daga barcin rana

Mutum na barci

Asalin hoton, OTHERS

Bayanan hoto, Masana sun bayar da shawarar yin barcin rana na ƙasa rabin sa'a a kullum
An wallafa

Samun ɗan lokaci don rintsawa a kai-a kai, yana da matuƙar alfanu ga lafiyar ƙwaƙwalwa kuma yana taimaka wa bunƙasar ƙwaƙwalwa tsawon lokaci, a cewar masu bincike daga Jami'ar University College London.

Rukunin masanan ya nuna cewa ƙwaƙwalwar masu taɓa ƙailula ko barcin rana tana kan ma'aunin kyubik sentimita 15, daidai da matakin da za ta iya rage tsufa da kusan shekara uku zuwa shida.

Sai dai kuma, masana kimiyyar sun bayar da shawarar cewar barcin, kada ya kai na rabin sa'a.

A cewar ƙwararrun, barcin rana yana matuƙar wahala ga ma'aikata a fannonin sana'o'i da dama, inda a wasu wuraren aikin ake ganin baiken masu taɓa ƙailula.

"Muna ba da shawara cewa kowa ne mutum zai iya samun amfani daga barcin," kamar yadda Dakta Victoria Garfield ta faɗa.

Ta bayyana sakamakon da aka gano da cewa "sabo ne fil kuma mai matuƙar ƙayatarwa".

Barcin rana, muhimmin abu ne ga bunƙasar rayuwar ɗan'Adam a lokacin da muke jarirai, sai dai muna girma, yana daɗa raguwa amma yakan sake ƙaruwa a lokacin da muka yi ritaya daga aiki, an ba da rahoton cewa kashi 27 cikin ɗari na mutanen da suka haura shekara 65 suna gyangyaɗawa da rana.

Dakta Garfield ta ce shawarar yin barcin rana "aba ce mai matuƙar sauƙi" idan aka kwatanta da rage kiba ko kuma motsa jika wadanda ke da "wahala a wajen galibin mutane".

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kaifin ƙwaƙwalwa bisa tsarin rayuwa yana disashewa yayin da shekaru ke ƙaruwa, amma shin ko barci yana taimakawa wajen yin kandagarkin cutuka kamar susucewar tunani, wannan wani abu ne da har yanzu yake buƙatar ƙarin bincike.

Lafiyar kwakwalwa tana da matuƙar muhimmanci wajen ba da kariya ga cutar tsananin mantuwa kuma larurar tana da alaka da katsewar barci.

Masana sun ba da shawarar cewa rashin isasshen barci yana lalata ƙwaƙwalwa a tsawon lokaci, kuma yana haddasa zogi sannan yana shafar jijiyoyin sadarwa tsakanin ƙwayoyin halittar jiki.

"Don haka, gyangyaɗi lokaci-lokaci yana iya kare mutum daga larurar mantuwa ko daina aikin ƙwayoyin halittun jijiyoyin laka ta hanyar rama tauyewar barcin da aka samu da dare," a cewar jami'ar bincike Valentina Paz.

Sai dai Dakta Garfield na da ra'ayin cewa maimakon ta samu wuri mai taushi ta kwanta ta yi ƙailula gwamma ta motsa jiki tsawon minti 30, amma ta ce za ta iya bai wa mahaifiyarta shawarar ta yi irin wannan barcin.

Ta yaya za a samu amsa?

Yin nazari a kan barci zai iya zama ƙalubale.

Barci zai iya inganta lafiya, sai dai saɓanin hakan ma gaskiya ne don kuwa ƙarancin lafiya za ta iya gajiyar da kai sosai ta yadda sai ka buƙaci ƙarin barci.

Masu bincike sun yi amfani da wata dabara wajen tabbatar da amfanin barci ga lafiyar jikin mutum.

Sun yi amfani da wata gagarumar hanyar gwaji bisa doron gudan halittar gado na DNA - da wani tsarin ƙwayar halittar gado da aka haife mu da shi.

Binciken da aka yi a baya ya shaida ɓantare 97 daga jikin gudan halittar gadonmu wanda ko dai yake sanya yiwuwar ƙara yin barci ko kuma ya ƙara wartsakar da mu tsawon rana.

Rukunin masu binciken ya ɗauki bayanai daga jkin mutum 35,000, 'yan shekara 40 zuwa 69, waɗanda suka cikin wani shiri mai taken UK Biobank Project kuma cikin sauƙi suka kwatanta ƙwayoyin halittun gadon "masu barcin rana" da "waɗanda ba sa barcin rana".

Sakamakon, wanda aka wallafa a mujallar lafiya ta Sleep Health, ya nuna bambancin kyubik sentimita 15 na girman ƙwaƙwalwa, daidai da tazarar tsufan shekara biyu da rabi zuwa shekara shida da rabi.

Jimillar zurfin ƙwakwalwar da aka samu ya kai kyubik sentimita 1,480, a binciken.

"Ina jin daɗin taƙaitaccen barci a ƙarshen mako kuma wannan binciken ya ƙara gamsar da ni cewa bai kamata na zama mai kasala wajen yin ƙailula ba, don kuwa yana ma iya bai wa ƙwaƙwalwata kariya," in ji Farfesa Tara Spires-Jones, daga jami'ar Edinburgh, kuma shugabar Ƙungiyar Masana Kimiyyar Jijiyoyin Laka ta Birtaniya.

Ta ce "abin sha'awa ne" yadda sakamakon binciken ya nuna "ƙari kaɗan amma kuma muhimmi a zurfin ƙwaƙwalwa" kuma ya "daɗa ba da bayanan da ke nuna cewa barci yana da muhimmanci ga lafiyar ƙwaƙwalwa".

Masu binciken kai tsaye ba su yi nazari game da yin barci mai nauyi da tsakar rana ba, amma sun ce kimiyya ta yi nuni da tasirin ɗan kishingiɗa na tsawon rabin sa'a.