Sai da asusun banki za ku iya samun duk wani tallafin kuɗi - Uba Sani

An wallafa

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya ce gwamnatinsa za ta ƙaddamar da wani shiri na buɗe wa mutanen karkara asusun ajiyar banki.

A wata tattaunawa da BBC, gwamnan ya ce za a yi hakan ne domin taimaka wa mutanen su samu tallafin da gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ƙuduri aniyar aiwatarwa.

Ya ce "Binciken da muka yi da kuma Bankin Duniya an gano cewa an gano cewa kashi 75 cikin ɗari na al'ummarmu na arewa maso yamma ba su da asusun ajiya."

Ya ƙara da cewa "Idan kuma mutum ba shi da asusun ajiya a banki ta yaya ne tallafin nan zai same shi?"

Gwamnan ya ce wannan lamari ne ya sanya akasarin tallafin da ake bayarwa a Najeriya ke zuwa ga mutanen kudancin ƙasar.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya dai ta ce za ta ɓullo da wasu shirye-shirye na sassauta raɗaɗin cire tallafin man fetur, bayan janye tallafin man da shugaba Bola Tinubu ya sanar a ranar da ya karɓ mulki.

Uba Sani ya ce idan aka ci gaba da yadda ake tafiya a haka ba tare da an ɗauki mataki ba, al'ummar arewacin Najeriya ba za su alfana da tallafin na gwamnatin tarayya ba.

''Yanzu idan aka ce za a raba wannan kudi da ake magana sama da dala miliyan 800 da za a karbo daga wajen Bankin Duniya, ina tabbatar maka da cewa daga karshe yan Arewa ba za su ci gajiyar ko kashi goma ba'' in ji shi.

Ya ce a kokarin gwamnatinsa na samar da ingantaccen tsari, za ta fara shiga yankunan karkara domin tabbatar da bude wa jama'a asusun banki, don samun saukin tafiyar da harkokinsu.

Gwamna Uba Sani na Kaduna ya yi bayani a kan ƙoƙarin da gwamnatinsa take yi wajen yaƙi da matsalolin tsaro da suka addabi jiharsa, da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Ɓangaren da ya fi fama da rikicin 'yan fashin daji a ƙasar. Gwamnan a wannan hira ta musamman da Sashen Hausa na BBC ya ce ya tuntuɓi takwarorinsa gwamnoni da jihohinsu ke fama da hare-haren 'yan fashin daji kuma sun cimma matsaya kan yadda za su tunkare su.

Sanata Uba Sani ya kuma ya tuntuɓi manyan hafsoshin tsaron Najeriya kamar babban hafsan tsaro na Najeriya, Manjo Janar Christopher Musa da babban hafsan sojojin saman ƙasar, Air Vice Marshal Hassan Abubakar don jin yadda gwamnatinsa za ta tallafa wa dakarunsu a ƙoƙarinsu na murƙushe 'yan fashin.

A halin da ake ciki a iya cewa cire tallafin man fetur din da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sanar ya jefa ƴan kasar da dama cikin tasku, la'akari da yadda farashin komai ya tashi, kama daga kan sufuri, kayan abinci, da sauran bukatun yau da kullum.

A yawancin jihohin kasar dai maganar da ake ana sayar da litar man fetur sama da Naira dari shida, sakamakon kari na biyu na baya-bayan nan da aka yi.

Sai dai gwamnatin Shugaba Tinubu na ganin cewa tsarin da ta bullo da shi na raba wa mutum miliyan 12 Naira dubu takwas zai taimaka wajen rage wa jama'a radadin taskun da suka shiga.

Masu suka dai na ganin cewa duk da cire tallafin ya zama dole a halin da ake ciki, gwamnatin ba ta yi kyakkyawan tsari na yadda za a aiwatar da shi ba.