Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Diago Jota ba zai buga gasar kofin duniya ba
Dan wasan tawagar Portugal, mai taka leda a Liverpool, Diago Jota, ba zai buga gasar kofin duniya ba, sakamakon raunin da ya ji in ji Jurgen Klopp.
Mai shekara 25 ya ji ciwo a wasan Premier League ranar Lahadi da Liverpool ta ci Manchester City 1-0 a Anfield.
Klopp ya ce '' Jota zai yi jinya mai tsawo, muna magana ta watanni da dama.''
Jota ya rubuta a kafarsa ta sada zumunta ''Bayan daren murna a Anfield tawa ta kare a mummunan yanayi, kuma daya daga mafarki na ya rushe gabaki daya.''
Dan kwallon bai fara buga Premier a bana ba, sakamakon jinya, wanda ya koma taka leda ranar 3 ga watan Satumba a wasan da Liverpool ta tashi 0-0 da Everton.
A cikin watan dan kwallon ya buga wa Portugal wasan da ta doke Jamhuriyar Czech 4-0, ya kuma ci kwallo daya daga ciki.
Ranar 20 ga watan Nuwamba za a fara gasar cin kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci.