Waiwaye: Kammala zaɓukan da ba a ƙarasa ba da iƙirarin ingantuwar tsaro a mulkin Buhari

An wallafa

Kamar kowane mako, a makon da ya gabata tsakanin 8 zuwa 15 ga watan Afirilu, abubuwa da dama sun faru a Najeriya ciki har da cika shekara tara da sace ƴan matan Chibok.

Buhari

Asalin hoton, prsidency

Kama Peter Obi a Birnin London

.

Asalin hoton, Getty Images

A makon da ya gabata ne, kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar LP ya ce jami’ai sun tsare tare da hantarar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi a birnin London.

Mai magana da yawun kwamitin kamfe na jam’iyyar LP, Diran Onifade ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a filin jirgin sama na Heathrow da ke London.

Ta ƙara da cewa jami’an shige da fice na Birtaniya ɗin ne suka titsiye tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar.

Diran Onafide ya ce hukumomi a Birtaniya sun tsare tare da yin tambayoyi ga tsohon gwamnan na jihar Anambra kan wani lamari da ya shafi wani mutum da ke yin sojan-gona da suna Peter Obi.

Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an sun sassauta wa Petetr Obi ne bayan wasu ƴan Najeriya da ke a filin jirgin sun sanya baki.

Peter Obi dai ya isa birnin na London ne domin bukukuwan Easter na mabiya addinin Kirista.

Jami’an shige da ficen sun yi bayani kan musabbabin tsare shi. Sun ce suna masa tambayoyi ne kan wani abu da ya jiɓanci sojan-gona.

Onifade ya ce illar sojan-gona ita ce akwai yiwuwar wanda ke sojan-gonar zai iya aikata laifukan da za a maƙala wa shi Peter Obi.

INEC ta ce Atiku bai cika sharuɗɗan zaɓe ba...

.

Asalin hoton, Reuters

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hukumar zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya INEC ta ce ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gaza cika sharuɗɗan da tsarin mulkin ƙasar ya gindaya kafin a ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu.

INEC ta bayyana haka ne a matsayin martani kan ƙorafe-ƙorafen da ɗan takarar ya shigar gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓe.

Ta dai buƙaci kotun ta yi watsi da ƙorafin da ɗan takarar ya shigar gabanta yana ƙalubalantar sakamakon zaɓen da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC nasara.

Hukumar ta ce Atiku ya gaza samun kashi 25 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa a aƙalla kashi biyu cikin uku na jihohin ƙasar 36 da kuma birnin tarayya Abuja, wanda hakan na cikin sharuɗɗan cin zaɓe a ƙasar.

Game da ƙorafin saɓa dokar zaɓe, INEC ta ce an gudanar da zaɓen ne bisa dokar zaɓen ƙasar ta 2022, ba tare da almundahana ba, kamar yadda masu ƙorafin suke zargi.

Hukumar zaɓen ta sake jaddada cewa Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC shi ne halastaccen zaɓaɓɓen shugaban ƙasar.

Kammala zaɓukan da ba a ƙarasa ba

.

A ranar Asabar ne, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa a Najeriya ta ƙarasa zaɓuka kusan 100 da suka rage, ciki har da na gwamnoni a jihohin Kebbi da Adamawa.

An bayyana zaɓukan a matsayin waɗanda ba su kammala ba ne, lokacin babban zaɓe na ƙasa ranar 25 ga watan Fabrairu da kuma na ranar 18 ga watan Maris.

Baya ga zaɓen gwamnoni a jihohin Adamawa da Kebbi, za kuma a kammala zaɓukan 'yan majalisar dattijai guda biyar da na 'yan majalisar wakilai 31.

Akwai kuma zaɓukan 'yan majalisun dokoki na jihohi guda 58 da aka ƙarasa duk a ranar ta Asabar.

INEC ta ce tuni aka kammala zaɓukan gwamnoni a jihohin Najeriya 26, da na 'yan majalisar dattijai 104, sai kuma 'yan majalisar wakilai guda 329, da zabukan 'yan majalisun dokokin jihohi 935, tuni kuma aka ayyana waɗanda suka yi nasara.

Akasari dai, an soke zaɓukan ne saboda tashe-tashen hankula da hargitsa zaɓe da kuma sauran matsaloli.

Shekara tara da sace ƴan matan Chibok

.

Asalin hoton, Getty Images

Shekara tara bayan sace ɗalibai mata kusan 300 daga makarantar sakandare ta Chibok, har yanzu babu labarin inda guda 96 suke.

A wata sanarwa da ƙungiyar Amnesty International ta fitar ranar Juma’a, a wani ɓangare na ranar tunawa da ranar da aka sace ɗaliban, ƙungiyar ta soki gwamnati bisa abin da ta kira ‘gaza kare su’.

A ranar 14 ga watan Afrilun shekara ta 2014, lokacin da rikicin Boko Haram ya yi ƙamari a yankin Arewa-maso-gabashin Najeriya, wasu mayaƙa suka kai farmaki a Makarantar Sakandare ta Chibok inda suka sace yara mata 276.

Daga baya sojoji sun samu nasarar ƙwato wasu daga cikin su, wasu kuma sun kuɓuta, yayin da ƙungiyar kuma ta sako wasu.

A sanarwar da ƙungiyar BBOG mai fafutikar ganin an ceto ɗaliban ta fitar domin tunawa da ranar, ta ce gazawar gwamnati wajen ceto yaran babban abin kunya ne.

Birtaniya za ta daina ɗaukan likitoci daga Najeriya

.

Asalin hoton, Science Photo Library

Birtaniya ta sanya sunan Najeriya a cikin jerin ƙasashen da ba za ta rinƙa ɗaukan likitoci da masu kula da masu rauni daga ƙasar ba.

Birtaniyar ta ɗauki matakin ne bayan sabunta ƙa’idojinta na ɗaukan ma’aikata daga ƙasashen ƙetare.

A yanzu sunan Najeriya ya faɗa cikin waɗanda aka sanya wa launin ja ko ɗorawa, wanda yake fitowa daga Hukumar Lafiya ta Duniya.

Jerin ƙasashen wanda WHO ke sabuntawa bayan shekaru uku na nufin cewa ba za a ɗauki jami’an lafiya daga irin waɗannan ƙasashe ba.

Hakan na nufin cewa Najeriya ba ta da isassun likitoci ko ma’aikatan lafiya da take buƙata, saboda haka bai kamata su riƙa samun raguwar ma’aikatan ba.

Sabunta jerin sunayen da Birtaniyar ta yi tamkar biyayya ce ga shawarar Hukumar Lafiya ta Duniya.

A yanzu Najeriyar ta shiga jerin ƙasashe 55 waɗanda ba za a iya ɗaukan jami’an lafiya daga cikinsu ba.

Sai dai kundin ƙa’aidojin aikin da Birtaniyar ta fitar ya ce ƙasashen da ke cikin jerin waɗanda lamarin ya shafa za su iya fita daga jerin bayan tattaunawar fahimtar juna tsakanin ƙasa da ƙasa.

Iƙirarin ingantuwar tsaro a mulkin Shugaba Buhari

.

Asalin hoton, Presidency

Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta ce shugaban ƙasar Muhamadu Buhari zai bar mulki a yayin da harkar tsaro da tattalin arzikin ƙasar suka inganta fiye da yadda ya same su a shekarar 2015, lokacin da ya hau karagar mulkin ƙasar.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar Femi Adesina ne ya bayyana haka a lokacin wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels a ranar Litinin, da daddare.

Ranar 29 ga watan Mayu ne dai shugaban ƙasar zai sauka daga mulki bayan kammala wa'adin mulkinsa na biyu.

Masu suka na zargin cewa harkar tsaron ƙasar ta taɓarɓare a ƙarƙashin mulkinsa, sakamakon zarginsa da son kai wajen naɗe-naɗen muƙamai musamman na tsaro a maimakon duba cancanta, ko tsarin raba daidai na muƙaman gwamnatin tarraya.

Adesina ya kare wannan mataki da cewa ana yin naɗin muƙaman manyan hafsoshin tsaron ƙasar ne bisa cancanta, domin a cewarsa bai kamata a siyasantar da harkar tsaro ba wajen naɗin muƙamai.

Mista Adesina, ya ce ko ma mene ne mutane za su ce, Buhari zai bar mulkin Najeriya a daidai lokacin da ƙasar ta inganta fiye da yadda ya same ta a shekarar 2015.