Tomiyasu ya gama buga wa Arsenal tamaula a bana

An wallafa

Dan wasan Arsenal, Takehiro Tomiyasu ya gama buga wasannin kakar bana, bayan da likitoci suka yi masa aiki a gwiwar kafarsa ranar Talata.

Gunners ta sanar cewar ya ji rauni ne a wasan da Sporting ta fitar da Arsenal a Europa League ranar Alhamis a Emirates.

Dan kwallon tawagar Japan, mai shekara 24 ya yi wasa 31 a Arsenal a kakar nan.

Gunners tana matakin farko a kan teburin Premier League da maki 69 da tazarar takwas tsakaninta da Manchester City ta biyu mai kwantan wasa.