Za a yi wa Neymar tiyata a gwiwarsa

Asalin hoton, Getty Images
Za a yi wa dan wasan gaban Brazil da Al-Hilal, Neymar tiyata a kafarsa ta hagu sakamakon raunin da ya ji a yayin da yake buga wa kasarsa wasa.
An fitar da dan wasan mai shekara 31 daga fili a kan gadon daukar marasa lafiya cikin hawaye yayin wasan da suka sha kashi a hannun Urugauy da ci 2-0 a ranar Talata.
"Lokacin bakin ciki da bacin rai," Neymar ya rubuta a shafinsa na Instagram.
"Nasan jajirtacce ne ni amma a wannan karon ina bukatar iyalina da abokaina tare da ni."
Babu wanda ya san tsawon wane lokaci Neymar zai yi jinya, ko kuma zai dauki watanni takwas ne zuwa 10 yana zaman zubar da hawaye.
"Brazil da kwallon duniya baki daya na bukatar lafiyar Neymar, saboda kwallon kafa na kara dadi idan yana cikin fili," in ji shugaban kwallon kafa na Brazil Ednaldo Rodrigues.
Dan wasan da ya fi yawan zura kwallo a tsakanin yan kwallon Brazil maza a tarihi yana ta fama da jinya a 'yan shekarun nan.

Asalin hoton, Getty Images






