Fuskoki masu zane-zane da mai rera waka na cikin hotunan Afirka na mako

Mace a gefen teku, dauke da buhu a hannunta a gaban wani kwale-kwale, sanye ta ke da  bular riga da adiko ruwan dorawa.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto, A ranar Asabar wata mace a garin Bargny mai tashar ruwa da ke gabashin birnin Dakar na Senegal tana tattara bola a ranar da aka ware domin tsaftar muhalli ta duniya…
An wallafa
Mace sanye da riga mai launuka daban-daban, fuskarta cike da murmushi, ta bude hannunta ta na kallon wani sashe da ya yi kama da teku.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto, Wadannan mutanen na cike da nishadi a gabar tekun Hout Bay a Cape Town na Afirka ta Kudu, yayin da ake ranar alkinta muhalli ta duniya...
 Sarauniyar kyau ta Masar, Hager Mohamed sanye da rigar jins da bakar doguwar riga, ta dauki hoton selfie a kusa da dalar tarkacen robobi, daure jikin rigar wani kyalle ne da aka rubuta: Sarauniyar kyau ta Masar 2022. and black dress taking a photo in front of a mountain of plastic rubbish. She is wearing a sash which reads: Miss Egypt 2022.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kai akwai tarin bola a wannan rana, sarauniyar kyau ta Masar, Hager Mohamed na daukar hoton selfi a kusa da dalar bolar robobi, a wani bangare na fafutukar da ake yi ta tsaftace kogin Nilu karkashin kungiyar VeryNile, aniyarsu ita ce gina dalar da ta fi kowacce tsaho a duniya da tarkacen da aka kwaso a bahar Nilu..
Ma’aikaci na zuba alawa mai launin dorawa cikin mazubin da zai ba ta fasali mai ban sha’awa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Amma a ranar Talata a wata masana’anta da ke birnin Alkahira, wani ma’aikaci ne ke dafa alawa a wani bangare na bikin Maulidin zagayowar haihuwar Annabi Muhammad SAW.
Wani mutum zaune cikin gonarsa, zaune a turbaya, gefensa da kwandunan Zaitun. Bishiyoyi sun yi kore shar, gwanin ban sha’awa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sai dai a wannan rana a dai Masar, babu tarin bola a wasu sassan kasar, amma abinci ya wadata, wani manomi ne zaune cikin gonar Zaitun a wajen kauyen al-Qatta da ke Giza....
Wizkid tsaye kan dandamalin otal din Accor da ke Faransa, sanye da kaya launin dorawa. Fitila mai launi mai kyau ta haska shi daga baya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Can a birnin Fari na kasar Faransa, fitaccen mawakin nan dan Najeriya Wizkid ne ya cashe a wani otal mai suna AccorHotels a ranar Juma’a, kwanaki biyu gabanin kaddamar da sabuwar wakarshi.
Mata biyu na dariya lokacin daukar hoto, hannunsu rike da tambula din lemo. Alamu sun nuna da daddare ne, an kunna fitila mai launin ruwan goro.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,  A Uganda kuwa wata dabdala aka shirya tare da cashewa a ranar Juma’a, wadannan matasan hudu sun halarci bikin kalankuwar wakoki na kwanaki hudu da ake kira Nyege Nyege, da ya hada dukkan mawakan yankin……
mat ana cashewa. Macen da ke tsakiya ta na sanye da bakin gilashi sai kyakyata dariya ta ke yi

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Gwamnatin Ugandan na barazanar hana yin bikin, kan cewa ana yada shan muggan kwayoyi da da Jima’i.
Wani mutum ya Kwame a gefen hoton Sarauniya, ana daukarsu hoto, a bayan shi kuma akwai katon katakon da ke alamta gicciye Isa al-Masihu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Idan muka kauce daga wurin dabdala kuwa, wani mutum ne yak e daukar hoto kusa da hoton Sarauniya Elizabeth ta biyu, a tsohuwar majami’ar All Saints Cathedral mai da dadden tarihi a birnin Nairobi ranar Lahadi, a wurin zaman makokin sarauniyar da aka yi a kasar.
Daya daga cikin matan na sanye da ruga mai launin bula, da adiko rowa, dayar kuma na sanye da wando dogo da riga bula.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wanshekare, mata biyu a birnin Johannesburg a Afirka ta Kudu na kallon yadda jana’izar kasa ta Sarauniya ke gudana.
Wani mutum sanye da hula mai launuka daban-daban, ya shafa farin fenti a fuskarsa. Idanunsa a rufe, da yanayin fuska mai ban dariya, ya ranbada janbaki.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An yi wani biki a birnin Cape Town ranar Laraba, bayan sanarwar dawo da bikin kalankuwa Minstrel Carnival da ake yi duk shekara, an dakatar da yi ne saboda bullar annobar korona….
Mace dauke da farantin tallan wani Alalen Oppa a wurin zanga-zangar. Kafadarta a waje, fuskarta dauke da alamar mamaki, yanayinta ya nuna ta saba ganin taro haka.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Can a Lagos din Najeriya ranar Litinin, an gudanar da zanga-zanga da kungiyar daliban jami’o’in kasar ta yi, kan fusatar kin janye yajin aikin malaman ASUU na watanni 7.
Wani mutum na kokarin daga karfe. Fuskar shi na dauke da yanayin da ke nuna dakyar ya ke dagawa

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Bari mu koma Afirka ta Kudu, a dai ranar Litinin, inda wannan mutumin ke wasan motsa jiki na daga karfe mai nauyi a Johannesburg. Wurin motsa jiki na The iKasi, wannan wuri ya taba kasancewa inda madugun yaki da wariyar kaunin fata kuma tsohon shugaban kasa Nelson Mandela ya taba zama....
Maza biyu na damben gargajiya, babu riga a jikinsu sun shafe jiki da farin alli.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,  Wasan damben gargajiya da aka yi a kasar Sudan ranar Juma’a, wadannan mazan na cikin wadanda suka yi damben kabilar Nuba.
Zane mai kayatarwa da launi daban-daban masu ban sha‘awa.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A Afurka ta Kudu ranar Alhamis, inda aka baje kolin zayyana daban-daban a gidan kason mata na da aka yi wa lakabin Keiskamma Art Project, da ke nuna al.’adun mutanen yankin.

Dukkan hotunan su na dauke da hakkin mallaka