Hukuncin kisa ga masu fataucin ƙwaya da sauya wa makarantu matsuguni a Kaduna

An wallafa

Yau ma kamar kowane mako, mun yi muku waiwaye kan muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da ya gabata

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da hukuncin kisa ga masu safarar ƙwaya

.

Asalin hoton, President of the senate/X

Bayanan hoto, Godswill Akpabio

A cxikin makon nan ne majalisar dattawan Najeriya ta amince da ƙudurin dokar hukuncin kisa ga masu safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar, bayan ƙudurin ya tsallake karatu na uku a zauren majalisar.

Majalisar ta amince ta ƙudurin bayan kwamitin majalisar kan ayyukan yaƙi da fataucin miyagun ƙwayyoyi, ƙarƙashin jagorancin Sanata Tahir Munguno ya gabatar da rahotonsa kan sabuwar dokar a zauren majalisar.

Yayin da take sake nazarin dokar, majalisar ta amince da dokar hukuncin kisan ne domin ƙarfafa ayyukan hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasar.

Majalisar wakilan Najeriya ta umarci CBN ya dakatar da harajin tsaron intanet

..

Asalin hoton, TWITTER/@FEMIGBAJA

Bayanan hoto, Majalisar dokokin Najeriya

A cikin makon ne kuma mambobin majalisar wakilan Najeriya suka umarci babban bankin ƙasar, CBN ya janye aiwatar da harajin tsaro na intanet da zai cire kashi 0.5 cikin ɗari a duk lokacin da aka tura kuɗi ta asusun banki.

'Yan majalisar sun bayyana matakin a matsayin abu mai sarƙaƙiya.

Wannan buƙatar dai na zuwa ne a matsayin martani ga wani ƙuduri kan buƙatar gaggawa na dakatar da gyara aiwatar da harajin tsaron intanet, wanda Kingsley Chinda ya gabatar.

A cewar ƴan majalisar, CBN ya janye takardar aiwatar da tsarin da ya fitar , sannan kuma ya fayyace tsarin yadda 'yan Najeriya za su fahimta.

Sirika da ‘yarsa sun gurfana a kotu

.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Hadi Siriia

A cikin makon ne kuma hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama Sanata Hadi Sirika da karin wasu, a gaban kotun birnin tarayya da ke Maitama.

EFCC ta gurfanar da Sirika ne bisa tuhume-tuhume shida, masu alaƙa da almundahanar kuɗi da ya kai naira biliyan 2.7, shi da wasu mutum uku, ciki har da 'yarsa, Fatima Hadi Sirika da Jalal Sule Hamma da kamfanin Al-Duraq Investment Ltd.

Bayan gurfanarwar ne kuma kotun da bayar da belinsu a kan kuɗi naira miliyan 100 kowannen su.

Jihar Kaduna za ta sauya wa makarantu 359 matsuguni saboda rashin tsaro

.

Asalin hoton, Uba Sani/X

Bayanan hoto, Gwamna Uba Sani

A cikin tsakiyar makon ne kuma gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana shirinta na sauya wa makarantu 359 matsuguni sanadiyyar ƙaruwar ayyukan ƴan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa a jihar.

Lokacin da yake magana a wani taro na masu ruwa da tsaki, Gwamna Uba Sani wanda ya samu wakilcin shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar, ya ce ayyukan ƴan bindiga kamar satar ɗalibai a Kuriga da wasu makarantu da ke faɗin jihar na dagula al'amura a ɓangaren ilimi.

Ya ce a dalilin haka ne yanzu haka gwamnati ta fara shirin sauya wa makarantu 359 matsuguni zuwa wasu wuraren da babu matsalar tsaro.

'Yan bindiga sun sace ɗaliban jami'a da dama a jihar Kogi

.

Asalin hoton, Confluence University

Bayanan hoto, Jamiar Kogi

A tsakiyar makon da muke bankwana da shi ɗin ne wasu 'yan bindiga ɗauke da makamai suka kai hari tare da yin garkuwa da ɗaliban jami'a tara a jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya, kamar yadda gwamnatin jihar ta tabbatar.

Sai dai ana fargabar adadin zai iya zarta hakan.

Rahotonni sun ce maharan sun dirar wa jami'ar Confluence University of Science and Technology ne da ke Osara–Okene da tsakar dare ranar Alhamis.

Bayan sun isa ne kuma suka dinga shiga ɗakunan ɗaliban da ke karatu domin shirya wa jarabawar da ke tafe kuma suka buɗe wuta a sama, suka tara wasu ɗalibai kuma suka wuce da su.

Bai kamata mu bari 'yan ta'adda su gagare mu ba – Sultan

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhamma Sa'ad Abubakar na uku ya shawarci 'yan Najeriya da su fahimci ƙalubalen da ke gabansu domin tunkarar su.

Sultan ɗin dai ya faɗi hakan ne yayin wata ziyara da ministan tsaron Najeriya, Muhammad Badaru ya kai masa a fadarsa a yau Juma'a.

"Bai kamata mu bari wani ya samu galaba a kanmu ba. Ministan tsaro ya san irin girman alhakin da ke rataye a wuyansa. Na kuma yi amannar cewa yana tuntuɓar masu ruwa da tsaki domin su taimaka masa . Muna aiki tare kuma ba za mu daina ba.