Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manchester City ta dauki Kalvin Phillips
Manchester City ta dauki dan kwallon Leeds United, Kalvin Phillips kan fam milayan 45.
Dan kwallon tawagar Ingila, mai shekara 26, ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka shida da kungiyar da ta lashe Premier League a kakar da ta wuce.
Dan wasan ya zama na uku da Pep Guardiola' ya dauka a bana, bayan Erling Haaland da kuma Stefan Ortega Moreno.
Phillips, wanda ya buga wasa 235 a kaka takwas a Leeds United, yana da sauran kaka biyu kwantiraginsa ya karkare a Elland Road, kafin cinikin nan.
Phillips ya fara yi wa tawagar Ingila tamaula a Satumbar 2020, an kuma bayyana shi a matakin dan wasan Ingila da ya taka rawar gani a 2020-21, wanda ya buga dukkan wasannin Euro 2020.
Philips muhimmin dan kwallo a karkashin koci, Marcelo Bielsa, ya yi wasa 37 a Championship a kakar 2019-20, inda Leeds ta koma buga Premier League, bayan kaka 16 rabonta da gasar.
Sai dai dan wasan ya sha jinya a kakar da aka kammala, amma ya buga wasa 20 a lik, sakamakon jinya da ya yi.