Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bayern Munich ta dauki matashi Mathys Tel daga Rennes
Bayern Munich ta kammala daukar matashi mai shekara 17, Mathys Tel daga Rennes.
Tel, wanda ya yi wa tawagar Faransa kyaftin ta matsa 'yan shekara 17 a lokacin da suka lashe kofin nahiyar Turai, shi ne na biyar da Bayern ta dauka a kakar nan.
Ya buga wa Rennes karawa 10 a babbar gasar tamaula ta Faransa da aka kammala.
Daraktan wasannin Bayern Hasan Salihamidzic ya ce ''Tel daya ne daga fitattun matasa a taka leda a Turai'' kuma ''kungiyoyi da dama na son daukar dan kwallon.''
Tuni Bayern ta dauki Matthijs de Ligt da Sadio Mane da Ryan Gravenberch da kuma Noussair Mazraoui.
Haka kuma Robert Lewandowski ya bar Jamus ya koma Barcelona da taka leda a kakar nan.