Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea za ta bayar da aron Santos ga Strasbourg
Chelsea na shirin bayar da aron Andrey Santos ga Strasbourg, mai buga gasar tamaula ta Faransa zuwa karshen kakar nan.
Santos ya saka hannu kan yarjejeniya a Chelsea a Janairun 2023 daga Vasco de Gama, daga baya ta bayar da shi aro a kungiyar.
Mai shekara 19 ya kuma buga wasannin aro a Nottingham Forest a farkon kakar nan, sai dai wasa biyu ya buga daga baya Chelsea ta yi masa kiranye a watan nan.
Kungiyar ta yanke shawarr kara bayar da aron Santos, domin ya kara samun gogewa, kafin ta fara amfani da ɗan kwallon.
Waɗanda suka mallaki Chelsea, a Yunin 2023, Todd Boehly da Behdad Egbahli su ne kuma suke da Strasbourg.
Haka kuma Chelsea ta bayar da aron Angelo a Santos, kungiyar da ta sayo ɗan kwallon, wadda Patrick Vieira ne ke horar da ita.
Ranar Laraba, Chelsea za ta fafata da Liverpool a wasan mako na 22 a Premier League a Anfield.
Liverpool ce ta daya a kan teburin Premier, yayin da Chelsea ke mataki na 10.