Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gadar Morbi : Yadda 'yan uwa uku suka rasa rayukansu a rana guda
- Marubuci, Daga Yogita Limaye
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Aiko rahoto daga, Morbi
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Da yammacin ranar Lahadi, Chirag Mucchadiya mai shakara 20 tare da 'yan uwansa Dharmik mai shekara 17 da Chetan mai shekara 15 sun tafi yawo tare.
Sun shaida wa mahaifiyarsu Kantaben cewa za su tafi "julto pul", ko gada mai reto - wata tsohuwar gada mai cike da tarihi da aka gina tun zamanin mulkin mallaka da masu tafiya a kafa kawai ke amfanI da ita.
An dai kyale mutane sake amfani da gadar ne a 'yan kwanakin da suka gabata bayan an yi wa gadar gyara na tsawon watanni.
Ranar da matasan suka bar gida na cikin ranakun bikin Diwali na mabiya addinin Hindi. Ana hutu a dukkan makarantu, kuma akwai iyalan da suke da irin wannan sha'awar ta ziyartar wannan gadar.
Chirag da 'yan uwan nasa biyu sun sayi tikitin hawa gadar kan rupee 17 kuma daga nan sai suka hau gadar mai tsawon mita 230.
Wani mutum mai suna Nitin Kavaiya ma na wurun tare da matarsa da 'ya'yansa mata biyu - daya mai shekara bakwai, dayar kuwa watanta bakwai da haihuwa.
Shi da iyalin nasa sun rika daukar hotuna.
Da kimanin karfe 6:30 na yammaci, sai suka sauka daga kan gadar kuma suka sami wani wuri a gabar kogin Macchu suka zauna.
"Akwai cunkoso a bisa gadar. Ina ganin akwai akalla mutum 400 zuwa 500 a kan gadar", inji Nitin.
"Na tafi wajen masu sayar da tikiti, kuma na sanar da su cewa ya kamata su rage yawan masu hawa gadar".
Bayan minti goma da yin wannan maganar, sai Nitin ya ji karar wani abu da kuma kukan jama'a.
Gadar ta karye a kusa da gabar kogin. Nitin ya ce, "Na ga mutane na fada wa cikin ruwan kogin kuma ba su taso ba bayan sun nutse."
Wasu sun yi sa'a makale wa jikin karafen gadar, amma akalla mutum 141 sun rasa rayukansu nan take, cikinsu har da 'yan uwan nan su uku, wato Chirag da Chetan da Dharmik.
Can a gidan wadannan 'yan uwa uku, wani cikin abokansu ya garzaya can kuma ya sanar da mahaifiyarsu Kantaben cewa gadar ta karye.
"Na rika yin kuka ina kiran 'ya'yana ta waya amma ban iya samunsu ba," inji ta.
Mijinta Rajesh ya garzaya can kuma daga can ya nufi asibitocin garin.
Da misalin karfe 11 na dare, ya gano gawarwakin Dharmik da Chirag a asibitin Morbi Civil.
Bayan sa'a hudu, da karfe uku ke nan, masu aikin ceto suka gano gawar Chetan.
A can gidan Mucchadiya kuwa, bakin ciki da tashin hankali ake ciki, yayin da 'yan uwa da makwabta ke tururuwar shiga gidan domin mika ta'aziyyarsu ga iyalan gidan da suka rage.
"Mun yi asarar dukkan 'ya'yanmu", imji Kantaben. "Mene ne ya rage mana kuma? Ni da mijina ne kawai muka rage."
Ba iyalan gidan Mucchadiya ne kadai suka rasa 'yan uwansu fiye da daya ba.
Hukumomi sun kama mutum tara kawo yanzu, ciki har da masu sayar da tikitin hawa gadar, da masu gadi da manajojin kamfanin Oreva, kamfanin da ya yi kwangilar gyaran gadar.
Nitin ya ce ba ya iya mantawa da abin, "A duk lokacin da na rufe idanuwa na, sai in rika ganin mutanen da ke fada wa ruwa daga kan gadar kuma in rika jin kukan mutanen da suka halaka a kogin."
"Saboda takaici ma na yaga tikitin da na saya na hawa gadar. Ba ni kadai ba ne ke jimami - dukkan mazauna wannan garin na cikin halin damuwa da fushi."
Sh ma Rajesh ya yi tsokaci, inda ya ce "kamata ya yi a gudanar da cikakken bincike, saboda idan ba a yi haka ba, jama'a za su ci gaba da mutuwa kamar yadda 'ya'yana suka mutu."