Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Bidiyon da aka ɗauka na ɗalibai tsirara' ya sa an rufe jami'a a India
An rufe wata jami'a a ƙasar India na tsawon mako guda bayan an gudanar da zanga-zanga mai ƙarfi kan zargin wata ɗaliba ta ɗauki wata ƴar uwarta ɗaliba bidiyo a asirce tana wanka.
Dubban ɗalibai ne a Jami'ar Chandigarh, wadda jami'a ce mai zaman kanta da ke arewacin Jihar Punjab suka yi zanga-zanga a ranar Lahadi, bayan an soma yaɗa jita-jita a cikin jami'ar da kuma kafofin sada zumunta cewa an wallafa bidiyon mata da dama suna wanka a intanet ba tare da saninsu ba.
Kamar yadda aka rinƙa bayar da bayanai a kafofin sada zumunta, ɗalibar da ake zargi ce ta yi duka bidiyon inda ta tura wa saurayinta.
Jami'ar da kuma ƴan sandan Punjab duk sun musanta waɗannan zarge-zarge.
Ƴan sandan a ranar Lahadi sun ce kawai su abin da suka gani shi ne bidiyon ɗalibar da aka kama, amma ƴan sandan sun ce tuni suka kama wadda ake zargin da saurayin nata kan zarge-zargen da suka haɗa da yaɗa hotunan sirri na mutane ba tare da izininsu ba.
"Ana nan ana bincike kuma wayar wadda ake zargi an tafi da ita domin bincikar ta," in ji Rupinder Bhatti wadda babbar jami'ar ƴar sanda ce wadda ke bincike na musamman kan batun.
Ms Bhatti ta kuma musanta wani rahoto na wata jarida da ke cewa wani daga cikin jami'an ƴan sanda a cikin sirri ya shaida musu cewa an ga bidiyon wata yarinya ta biyu a cikin wayar wadda ake zargin.
Ɗaliban sun kammala zanga-zangar da suke yi tun a ranar Lahadi bayan da hukumar gudanarwa ta makarantar da kuma ƴan sandan suka amince da wasu buƙatunsu.
Sai dai duk da haka wannan batun ya zama abin tattaunawa a kafafen sada zumunta wanda a nan ne aka soma yaɗa wasu labaran ƙarya kan wannan batun.
Pawan Duggal, wanda masani ne kan dokokin da suka shafi intanet ya bayyana cewa wannan batun ya fito ƙarara da ƙalubalen da ke jami'o'i ke fuskanta idan ana batun watsa labaran ƙarya.
"Dole ne a fito da sabbin hanyoyi - batun rufe jami'o'i ba hanya ba ce mai ɓullewa," in ji shi.
Wasu ɗalibai mata a jami'ar sun shaida wa BBC cewa duk da hujjojin da ake da su a ƙasa - wasu sun ce ba su ji daɗin yadda hukumomi suka ɗauki wannan lamarin ba.
Takamaimai me ya faru?
Zanga-zangar wadda aka fara da yammacin ranar Asabar ta ƙara ƙamari washe gari inda ƴan ƙasar suka sha mamaki.
Wannan batun ya karaɗe labarai da shafukan sada zumunta.
BBC ta tattauna da wasu ɗalibai biyar a jami'ar - wasu huɗu sun yi magana inda suka buƙaci a ɓoye sunansu.
Ɗaya daga cikinsu, Shikha (an sauya sunanta), ta bayyana cewa tana cikin bayi a ranar Asabar da dare inda ta ga tarin wasu ɗalibai mata suna gudu zuwa waje.
Kwatsam sai wata ƙawarta ta faɗo tana karkarwa, inda ta ce ta ji labarin wata ɗaliba ta kashe kanta bayan an wallafa bidiyonta a shafukan sada zumunta.
Ko da suka sauka ƙasa domin su ga abin da ke faruwa, Shikha sai ta ce sai ta ga ana rikicin da ba ta taɓa gani ba - wasu mata na ihu inda ake ci gaba da taruwa.
Shikha ta bayyana cewa sai kuma daga baya wata ƙawarta ta shaida mata cewa wata sabuwar zuwa jami'ar ce ta ɗauki bidiyon wasu mata suna wanka, lamarin da ya jawo zanga-zangar.
Jami'ar a wata sanarwa ta bayyana cewa: "Babu wasu bidiyo da aka gano na wasu ɗalibai irin waɗanda ake yayatawa sai dai wani bidiyo da yarinyar da ake zargi ta ɗauka da wayarta inda ta tura wa saurayinta.
"Sai dai Shikha da sauran ɗalibai huɗu sun shaida wa BBC cewa suna kyautata zaton jami'ar da kuma ƴan sanda suna ɓoye wani abu.
Suna zargin yarinyar da ake zargin ta ɗauki bidiyon wasu ɗaliban na daban - sai dai dukansu babu ɗaya daga cikinsu da ya ga irin wannan bidiyon ko kuma sanin wani da ya ga bidiyon.
Ms Bhatti ta sake jaddada wa BBC cewa wadda ake zargin wadda aka kama ta musanta ɗaukar bidiyon wata ɗaliba ƴar uwarta kuma Ms Bhatti ɗin ta ƙara da cewa ba su gano wasu hujjoji ba ko kuma wasu bidiyoyi ba.
Haka kuma BBC ta tura tambayoyi zuwa adreshin email na jami'ar amma babu amsa daga jami'ar tukuna.
Me ya faru a shafukan sada zumunta?
A lokacin da zanga-zangar ke ci gaba, an soma yaɗa jita-jita a shafukan sada zumunta.
Saƙonni da dama da aka wallafa sun yi iƙirarin cewa wasu ɗaliban sun yi niyyar kashe kansu kan cewa an tona musu asiri - haka kuma wasu sun yaɗa hoton wata yarinya da ba a san wacece ba wadda aka saka cikin motar kwana-kwana ta asibiti.
Sai dai jami'ar da kuma ƴan sandan ƙasar duk sun musanta wannan batu sai dai yan sandan sun tabbatar da cewa akwai wata ɗaliba da ta suma saboda damuwa.
A shafin Twitter wasu masu amfani da shafin sun gargaɗi wasu kan cewa ka da su kuskura su yaɗa bidiyon idan aka tura musu, sai dai babu wanda ya tabbatar da ya sa samu bidiyon.
Haka kuma ba a wallafa bidiyoyin ba a shafukan sada zumunta.
Sai dai masu amfani da shafukan da dama sun wallafa bidiyoyin ɗalibar da ake zargi - inda masu kula da ɗakunan kwanan ɗalibai suka rinƙa mata faɗa wasu kuma ƴan uwanta ɗalibai suna fito-na-fito da ita.