Umtiti ya koma Lille daga Barcelona

Samuel Umtiti

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Mai tsaron bayan tawagar Faransa, Samuel Umtiti ya koma taka-leda a Lille daga Barcelona.

Mai shekara 29, wanda ya buga wa Lyon tamaula kafin ya koma Barcelona, ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyu da kungiyar da ke buga Ligue 1.

Umtiti - wanda ya taɓa lashe Kofin Duniya - ya sha fama da jinya kusan shekara hudu, hakan ya sa aka bayar da aronsa da Lecce a kakar da ta wuce.

''Tun farko na so komawa Lyon, daga baya na amince na taka-leda a Lille, wadda ita ce ke bukatar na buga mata tamaula,'' in ji dan wasan.

Mai tsaron bayan ya fara taka leda a Lyon tun daga matasan kungiyar, wanda ya lashe babban kofin gasar kwallon kafar Faransa a 2012.

Tun farko an sanar cewar dan kwallon wanda aka haifa a Kamaru zai koma Lyon ne, amma daga baya aka ce ya zabi yi wa Lille tamaulo.

Umtiti shi ne ya ci wa Faransa kwallo a karawa da Belgium a daf da karshe a 2018, sai dai rabon da ya yi wa tawagar wasa tun 2019.