Jirgin da zai kai tawagar Gambia Afcon ya yi saukar gaggawa

An wallafa

Kocin Gambiya Tom Saintfiet ya ce "ƙiris ya hana tawagar Gambiya ta mutu" a hanyarta ta tafiya gasar kofin Afrika ta 2023 da za a yi a ƙasar Ivory Coast.

Tom Saintfiet ya ce hakan ya faru ne saboda ƙarewar iskar shaƙa da aka fuskanta a cikin jirgin lokacin da ya tashi.

Jirgin saman Air Cite d'Ivoire ya yi saukar gaggawa ne bayan mintina da tashin da ya yi daga Banjul babban birnin Gambiya a ranar Laraba.

Kocin ya yi amannar an fuskanci ƙarancin iskar shaƙa, inda ya ce hakan ya sa wakilan tafiyarsu da dama suka fara barci.

Kocin ya yaba wa tunani da matakin gaggawa da matuƙan jirgin suka yi na dawo da su inda suka tashi.

Jami'an jirgin sun tabbatar da faruwar wannan matsala a jirgin.

Cikin wata sanarwa da kamfanin jirgin ya fitar ya ce tuni aka shawo kan wannan matsala, sai dai an soke tashin jirgin baki daya.