Za a fitar da jadawalin gasar Firimiyar Ingila

Asalin hoton, Getty Images
Za a fitar da jadawalin gasar Firimiyar Ingila, kakar 2024-25 a ranar Talata.
Ƙungiyar Ipswich Town za ta jira ta ga wace ƙungiya ce za ta kara da ita a karon farko cikin shekara 22, bayan da ta samu komawa cikin gasar.
Ita kuwa Leicester, wadda ta lashe gasar Championship da kuma Southampton wadda ta lashe wasan fitar da gwani za su dawo gasar bayan kaka ɗaya da suka bar ta.
Sai kuma Machester City wadda za ta shiga kakar da fatan lashewa a karo na biyar a Jere.
Sabbin masu horaswa
Ya zuwa yanzu ƙungiyoyi huɗu sun naɗa sabbin masu horaswa da za su taka rawa a gasar mai shigowa.
Fabian Hurzeler na Brighton, Enzo Maresca na Chelsea, Arne Slot na Liverpool sai Julen Lopetegui na West Ham – kuma ana sa ran Leicester ta zama ƙungiya ta biyar da za ta kawo sabon kocin fil.
Yaushe za a fara gasar?

Asalin hoton, Getty Images
Gasar Firimiyar Ingila ta kakar 2024-25 za ta fara ne a ranakun ƙarshen mako na 17 da 18 ga watan Agusta.
Za a yi artabu a ƙarshen makonni 33, sai wasanni hurhuɗu na tsakiyar mako da kuma karawar ranar hutu guda ɗaya.
Za a buga wasannin ƙarshe ne a ranar 25 ga watan Mayu, 2025, inda a ranar za a fara dukkanin wasannin a lokaci ɗaya.











