Me kuke son sani kan Premier ta baɗi da za a fara 2024/25?

Asalin hoton, Getty Images
Bayan da aka karkare gasar Premier League ta 2023-24, yanzu saura kasa da mako 10 a fara kakar 2024/25.
Manchester City ta lashe kofin da aka kammala kuma na hudu a jere da ta lashe ba wadda ta kai ƙungiyar Etihad wannan bajintar.
Koda yake a ranar karshe aka tantance mai kofin, inda Arsenal ta yi ƙokarin ɗaukar kofin babbar gasar tamaula ta Ingila, wadda rabon ta da shi yanzu shekara 21.
Ga jerin kwanakin da ya kamata ku sani kan Premier League?
Yaushe ne za a fara Premier League ta badi?
Za a fara wasannin farko a Premier League kakar 2024-25 a karshen makon 17-18 ga watan Agustan 2024.
Za kuma a yi mako 33 ana gumurzu da karo hudu da za a yi fafatawar tsakiyar mako da kuma hutu daya da za a yi lokacin gudanar da wasannin.
Haka kuma da yake a tsakiyar watan Agusta za a fara gasar, an kuma tsara yin hutu a lokacin hunturu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Haka kuma an tsara yadda za a kaucewa wasa da yawa a lokacin bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara - babu ƙungiyar da za ta yi wasa tsakanin kasa da awa sittin da wanda ta buga a baya.
Za a karkare gasar Premier League ta kakar da za mu shiga ranar Lahadi 25 ga watan Mayun 2025, kuma za a buga wasannin karshen a rana daya a kuma lokaci ɗaya.
Yaushe ne za a fitar da jadalin Premier League ta 2024/25?
Ranar Talata 18 ga watan Yuni ake sa ran fitar da jadawalin Premier League ta baɗi.
Za kuma a fitar da dukkan wasannin da ƙungiyoyin za su yi da karawar da zasu karɓi bakuncin da wasannin da za a buga a waje.
Haka kuma za a bar lokacin da za a fafata a FA Cup da League Cup da wuraren da za a buga gasar zakarun Turai ta kakar baɗi.
Yaushe ne za a buɗe kasuwar saye da sayar da ƴan ƙwallo?
Za a bude kasuwar saye da sayar da ƴan ƙwallo ranar Juma'a 14 ga watan Yunin 2024, kuma a ranar za a fara gasar cin kofin nahiyar Turai, wato Euro 2024.
Kenan za a rufe kasuwar har zuwa karshen watan Agusta, wato ranar Juma'a 30 ga watan Agustan 2024.
An kuma tsara yadda kasuwar bana za ta ci, domin kula da yadda za a fara sauran gasar kasashen Turai.
An cimma yarjejeniyar kammala kasuwancin ƴan ƙwallon a karshen watan Agusta, bayan da aka tattauna tsakanin Premier da Bundesliga da Serie A da La Liga da kuma Ligue 1.











