Magoya bayan Tottenham sun yi zanga-zanga kan mai ƙungiyar Levy

Asalin hoton, Getty Images
Sama da magoya bayan Tottenham 1,000 ne suka yi zanga-ganga kan shugaban ƙungiyar, Daniel Levy kafin wasa da Manchester United a Premier ranar Lahadi.
An yi ta kuwa da cewar ''Levy ya bar ƙungiyar da kuma ''Enic ya bar Tottenham'' yayin da magoya baya suka rinka ɗaga tuta a kusa da sitadiya, wadan da ke kiraye-kirayen a kawo canji.
An kuma tsara yin zaman durshan da zarar an tashi wasan Premier a karawa da United, inda magoya baya suka bukaci da kowa ya tsaya a filin wasan Tottenham.
An kafa ƙyalle a wajen zaman masu gida da wajen zaman baki da aka rubuta sakon cewar ''lokacin canji ya yi'' domin ''shekara 24 an sauya masu horarwa 16 da lashe kofi ɗaya.''
Kafin Tottenham ta buga wasa da Manchester United ranar Lahadi tana ta 15 a teburi, wadda ta ci wasa ɗaya daga takwas baya da ta fafata.
Tottenham ta lashe League Cup a 2008 - tun bayan da Levy da Enic suka mallaki ƙungiyar daga Sir Alan Sugar, kusan shekara 25 da ta wuce.
To sai dai Tottenham ita ce kan gaba a samun riba a Premier League a tsawon shekarun, inda Levy ya samar da £1.2bn da aka gina katafaren filin wasa da kasaitaccen wajen atisaye.
BBC ta bayar da rahoto daga majiya da ta samu daga Tottenham cewar Levy ya ji takaicin zanga-zangar da rashin kokarin ƙungiyar a kakar nan.











