Dole a yi bincike kan kisan Falasdinawa a wajen rabon tallafi — Antonio Guterres

Antonio Guterres
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Babban sakatare a Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga da a gudanar da cikakken bincike a kan kisan Falasdinawa a cibiyar da ake rabon kayan tallafi a Gaza.

Ganau sun rawaito cewa an bude musu wuta a yayin da suke jiran abinci daga cibiyar da ke Rafah inda gidauniyar nan da ke samun goyo bayan Amurka da Isra'ila ke rabon tallafi.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce asibinta ya karbi mutum 179 da suka samu rauni inda 21 daga cikinsu sun mutu.

Hukumar tsaro ta farin kayan Hamas ta ce mutum 31 ne suka rasa ransu.

A ranar Lahadi, 1 ga watan Yunin 2025, rundunar sojin Isra'ila ta musanta cewa dakarunta sun bude wa fararen hula wuta a kusa da kuma harabar inda ake rabon kayan tallafi tana mai cewa duk wani rahoto akan cewa sojojinta sun kashe mutane a wajen ba gaskiya bane

Gidauniyar ta ce ya kamata a rinka tabbatar da abu kafin a furta.

Isra'ila ta hana kafafan yada labarai ciki har da BBC shiga cikin Gaza abin da ya sa tabbatar da abubuwan da ke faruwa a Gazan zai yi matukar wuya.

Babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniyar cikin wata sanarwa yace " Ya kadu da rahotannin da ke cewa an kashe tare da raunata Falasdinawa a yayin da suke jiran tallafi a Gaza."

Ya kara da cewa," Ina mai kira da gaggauta gudanar da cikakken bincike akan wannan lamari domin a gano ainihin wanda ya aikata wannan aika aika."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta mayar wa da babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya kakkausan martani a wani sako da ta wallafa a shafinta na X inda ta soke shi tana mai cewa mai ya sa bai ambaci Hamas ba sai sojojin Isra'ila.

A jiya Litinin shugaban hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya Volker Turk, ya shaida wa BBC cewa hanyar da ake bi wajen rabon kayan tallafi ba daidai ba ce kuma ba za a amince da ita ba.

Ya ce " Ina ganin abin da ake nunawa bai kamata ba ga fararen hula.Yanzu ace mutanen da ke matukar bukatar abinci da maganni kusan watanni uku wai sune zasu rinka gudu don karbar abincin sannan ga wulakanci kafin su samu?" Wannan sam ba a yi wa mutanen adalci ba kuma take hakkin dan adam ne.

Kungiyar likitocin agaji ta Medicins Sans Frontiers, ta ce tawagarta da ke asibitin Nasser a Khan Younis ma na yi wa mutanen da suka samu munanan raunuka magani inda wasu daga cikinsu ke halin rai kwa-kwai mutu kwa-kwai.

A wani labarin kuma, an sake kashe mutane a inda ake rabon kayan tallafi a kudancin zirin Gaza.

Kakakin hukumar tsaron farin kaya ta Hamas ya ce sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa 19, ciki har da mata, bayan sun bude wuta da tankokin yaki da jirage marassa matuka kan dubban Falasdinawa da suka taru suna jiran a ba su damar shiga sansanin da ake raba agajin.

Ma'aikatar lafiya ta Gaza kuma na cewa adadin mutanen da aka kashe ya kai 24, haka ma wasu kafofin yada labarai a Gazan ke cewa.

Isra'ila na cewa sojojinta na harbi ne idan suka fuskanci wani yanayi ko alamar barazana.