Trump ya umarci bayyana takardun sirri kan kisan Kennedy da Luther King

An kashe Shugaba Kennedy lokacin da kwambar motocinsa ke wucewa a Dallas a 1963.

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umarnin bayyana takardun sirri na bayanin kisan kai uku da aka yi da suka fi daukar hankali a tarihin kasar - kisan Shugaba John F Kennedy, da kaninsa Robert F Kennedy, da kuma dangwagwarmaya Martin Luther King Jr.

"Mutane da yawa sun dade suna jiran ganin wannan, tsawon shekaru, tsawon gomman shekaru,'' Trump ya gaya wa manema labarai a ofishinsa a ranar Alhamis. ''Kuma za a bayyana komai."

Umarnin ya sa manyan jami'ai su fitar da tsarin da za a yi amfani da shi wajen bayyana takardun cikin kwana 15. To amma fa wannan ba tabbas ba ne cewa hakan zai faru fa.

An kashe Shugaba John F Kennedy ne a Dallas a 1963. Shi ma kaninsa Robert F Kennedy an kashe shi lokacin da yake neman takarar shugaban kasa a California a 1968, wata biyu kacal bayan kisan Martin Luther King - dangwagwarmaya da ya fi fice a Amurka, wanda aka kashe a birnin Memphis, da ke jihar Tennessee.

An fitar da dama daga cikin takardun binciken kashe-kashen tun a shekarun, kodayake har yanzu akwai dubbai da ba a bayyana su ba, musamman ma na kisan Shugaba JF Kennedy.

Wani tsohon sojan Amurka na rundunar zarata - Lee Harvey Oswald, wanda ya sauya sheka zuwa Soviet Union, daga baya kuma ya koma Amurka, shi ne ya harbe Shugaba John F Kennedy.

A binciken da gwamnati ta yi ta ce, ta gano cewa, Oswald ya aikata hakan ne shi kadai, ba tare da taimakon wani ba.

To amma kuma wasu tambayoyi da dama sun biyo baya da daewa a kan kisan, kuma hakan ya sa ake jita-jita a kan yuwuwar hannun jami'an gwamnati da wasu masu juya al'amura da sauran wasu mutane da ake ganin na da muguwar aniya a kan shugaban.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kuri'ar ra'ayin jama'a da aka yi a gomman shekaru baya ta nuna cewa yawancin Amurkawa ba su yarda cewa Oswald shi kadai ya aikata kisan ba.

A 1992, majalisar dokokin Amurka ta zartar da wata doka da ta bayar da damar fitar da dukkanin takardun da ke da alaka da binciken cikin shekara 25.

Dukkanninsu Trump a wa'adinsa na farko da kuma Shugaba Joe Biden sun saki tarin takardu na binciken kisan Shugaba Kennedy , to amma har yanzu akwai dubbai daga cikin miliyoyi da har yanzu ba a bayyana ba.

A lokacin mulkinsa na farko Trump ya yi alkawarin fito da dukkanin takardun sirrin fili, to amma ya sauya shawara bayan da jami'an hukumar leken asiri ta Amurka CIA da hukumar binciken manyan laifuka ta kasar FBI suka shawo kansa da cewa ya kamata a bar wasu takardun na sirri kada a bayyana su.

Umarnin da Trump din ya bayar a yau, ya nuna cewa ci gaba da barin takardun binciken cikin sirri ba abu ne da ya dace da muradun al'umma ba.

''Domin nuna aniyarsa ta yin abin da gaske yana da kyau da shugaban ya rubuta alkawarin. Wannan yana da kyau,'' in ji Jefferson Morley, tsohon editan jaridar Washington Post, kuma kwararre kan kisan JFK sannan kuma editan jaridar intanet kan Shugaba Kennedy - JFK Facts.

"To amma cikakkun bayanan da aiwatarwar su ne komai. Wannan abu ya fara ne yanzu. Abin da ba a sani ba takamaimai shi ne yadda za a aiwatar da abu,'' in ji shi.

Takardun da aka fitar kwanan nan sun bayyana sababbin bayanai a game da kisan ciki har da tsananin sa-ido da lura da Oswald da hukumar CIA ta yi.

Lee Harvey Oswald bayan da 'yansandan Dallas suka kama shi a 1963. Wani dan-bindiga ne ya harbe Oswald tun kafin a gurfanar da shi a gaban kotu

Asalin hoton, Reuters/Dallas Police Department

A 2023, Paul Landis, wani tsohon jami'in leken asiri mai shekara 88, wanda ya ga kisan shugaban a kusa da kusa, ya ce ya dauki harsashi daga motar shugaban kasar bayan an harbe shi.

Kwararru sun ce wannan bayanin ya rikita bayanin hukuma cewa harsashi daya aka yi amfani da shi wajen harbin shugaban da gwamnan Texas John Connally, wanda ke cikin mota tare da shugaban kuma ya tsira daga harbin.

Mista Morley ya ce sababbin bayanai sun kara sanya kokwanto a kan bayanin cewa Oswald shi kadai ya yi kisan kuma ya yi hasashen cewa sakin takardun binciken gaba daya zai sa mutane su kara sanin ainahin abin da ya faru.

To amma ya ce ba lalle ba ne a samu cikakkiyar sheda ta yankan shakku, kuma hukumar CIA da sauran jami'an tsaro za su iya matsawa a kan a sirrinta wasu abubuwan.

"Wannan labarin bai kare ba," ya ce.

A lokacin sanya hannu a umarnin fitar da takardun binciken a fadar gwamnatin Amurka - White House, a ranar Alhamis , Trump ya sa a bai wa dan RFK wato kanin JFK, Robert F Kennedy Jr kuma mutumin da Trump din ya zaba a matsayin sakataren ma'aikatar lafiya, biron da ya yi rubutun da shi.

daman da dadewa RFK Jr na nuna shakku a ka bayanan hukuma a kan kisan wan mahaifinsa (Shugaba Kennedy ) da kuma mahaifinsa, Robert F Kennedy.

Wani Bafalasdine ne Sirahn Sirhan wanda ke bakin ciki kan goyon bayan da Amurka ke bai wa Isra'ila ya kashe mahafin nasa ne - Kennedy Sr a wani dakin rawa a Los Angeles.

RFK Jr ya yi magana da Bafalasdinen a gidan yari, kuma ya ce shi kam bai yadda cewa mutumin ne ya kashe mahaifinsa ba, kodayake wasu iyalan gidan Kennedyn sun yi watsi da wannan magana.

Shi kuwa dangwagwarmaya - Martin Luther King Jr wani mai tsattsauran kishin fara fata ne - James Earl Ray ya harbe shi. Iyalan dangwagwarmayar sun yi zargin cewa mutumin ba shi kadai ya kitsa kisan ba - suna ganin akwai wasu da yawa da suke da hannu a ta'asar.