Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Isra'ila ta kai hare-hare kan wuraren da shugaban Hezbollah yake a Lebanon
Jiragen sama na yaki na Isra’ila sun kaddamar da sababbin hare-hare a kan wasu gine-gine a babban birnin Lebanon Beirut, inda sojin suka ce Hezbollah na tara makamai.
An ji karar fashewa a yankin wajen kudancin birnin, inda sojin Isra’ilar suka umarci mazauna wasu gidaje uku su fice.
Zuwa yanzu ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta tabbatar da mutuwar mutum shida da jikkatar sama da 90.
Hotunan da ake gani daga babban birnin na Lebanon na nuna yadda hayaki da wuta ke tashi sama a cikin dare, yayin da jiragen sama na yaki na Isra’ila ke ta kai hare-haren kashi na biyu a kan wuraren da ke wajen kudancin Beirut din, inda ta ce wurare ne da kungiyar Hezbollah ke boye makamai.
Tun da farko kafin wannan harin na biyu, Isra’ilar ta kai wasu jerin hare-hare sama da ashirin, tsawon sama da sa’a biyar, tana kaiwa, inda ta ruguje gine-gine da dama – inda wani mazaunin yankin ya kwatanta lamarin da girgizar kasa..
Dubban mazauna yankin sun tsere daga gidajensu inda suka fake a wuraren shakatawa da filaye da gefen tituna da bakin teku.
Isra’ilar dai ta ce ta kai hari kan hedikwatar Hezbollah, yayin da wasu rahotanni ke cewa ta hari jagoran kungiyar Hezbolla ne, Hassan Nasralla, amma ba a san ko an same shi a hare-haren ba.
Masu aikin ceto na ta tona buraguzai domin gano wadanda ke da sauran numfashi.
Ofishin jakadancin Iran- kasar da ke mara baya ga Hezbollah – ya kira harin da cewa lamari mai hadarin gaske da zai sauya al’amura.
Da yake magana a wani taron manema labarai Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce, gwamnatin Amurka, ta yi amanna cewa diflomasiyya ita ce hanyar da ta fi dacewa ta samun mafita kan rikici.
Blinken, ya ce, ''Halartacciyar manufa ce kuma mai muhimmanci ga Isra’ila ta sake samar da muhallin da mutane za su iya komawa gidajensu. To amma maganar ita ce, wace hanya ce ta fi dacewa da cimma hakan. Wace hanya ce mafi dorewa da za a yi hakan. Mun yi amanna haka kuma kasashe da dama da suka bi sahunmu na kiran da a dakatar da bude wuta tsawon kwana 21, mun yi amanna hanyar da ta fi dacewa wajen cimma hakan ita ce ta diflomasiyya, ta dakatar da bude wuta sannan a cimma yarjejeniya.’’
Rundunar sojin Isra’ilar ta ce ta kuma kai hari kan wasu wuarre a birnin Tyre da ke kudancin Lebanon din, inda ta ce ta hallaka kwamandojin kungiyar ta Hezbollah da dama.
Duk da kiraye-kirayen da hukumomi da kasashen duniya ke yi na kada rikicin ya fadada, wadannan hare-haren na yanzu na nuni da cewa batun dakatar da bude wuta ba ya gaban Isra’ila a yanzu.