Kusan Malamanku tare da Malam Ibrahim Adam al-Madani

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon.
An wallafa

Daya daga cikin fitattun malamai a Najeriya Malam Ibrahim Adam Usman ya ce an taɓa yi masa tambayar da sai da ya kusan kwanaki kafin ya yi tunanin yadda zai bayar da fatwarta.

Cikin wata tattaunawa da BBC Hausa ta cikin shirin Kusan Malamanku, Malam Ibrahim Adam wanda aka fi sani da al-Madni, ya ce tambayar ita ce wadda wani "aboki ya kwanta da matar abokinsa" lokacin da maigidan baya nan.

Ko da yake malam ya ce an fi yi masa tambaya a kan lamuran da suka shafi aure da kuma zamantakewar auren, amma wannan yana yawan girgiza shi duk lokacin da ya tuna.

Malam Ibrahim wanda aka haifa a ranar 24 ga watan shida 1977 a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya , ya ce duk da cewa mahaifinsa ba malami ba ne ɗan kasuwa ne, amma Allah ya sa yana da sha'awar karatu, wanda hakan ya sanya tun da suka tashi suke fagen neman ilimi.

Mahainsa ya sanya shi makarantar Islamiyya, amma tasirin abokai ya sanya yake bin abokansa zuwa makaratarsu ta allo.

Ya yi ɓangaren karatun boko amma ya tsaya ne a iya matakin sakandire, sai dai a bangaren karatun addinin ya tiƙe har digiri na biyu, wanda kuma a yanzu haka yana kan yin na uku.

Ina da malamai ciki da wajen Najeriya

Na yi karatu a gaban malamai da yawa, kuma wasu ma ba zan iya tuna su ba, in ji Malam Ibrahim.

"Cikin Malaman da na tasirantu da su akwai Malam Rabi'u Daurawa da Muhammadu mai Ti da Malam Yahaya Muhammad al-Salafy, akwai Muhammad Bin Uthman da margayi Malam Ja'afar Mahmood Adam,

A Madina na yi karatu a wajen Farfesa Sulaiman Ruhaili wanda a hannunsa na yi karatun tauhidi, Sheik Abdul-Muhsunil Abbad, Sheik Abdul'aziz Ɗuwaiyyan.

Ina fatan waɗan nan bayin Allah, ubangiji ya saka musu da alkhairinsa.

Na fi son karanta Suratu Nahli

Malan ya ce ya samu damar karatun al-Ƙur'ani mai girma kuma na fuskanci wurare masu wuya kamar yadda kowa yake fuskanta lokacin hadda.

"Al-Ƙur'ani buwayayye ne, ba na mantawa ana cewa Suratu Nahli ga daɗi ga wahala" dan haka an sha wuya a cikinta.

Ina yaro ma haka na fuskanta a Suratu Buruj, amma duka daga baya an wuce waɗan nan lamura, in ji Malamin.

Ya ƙara da cewa ya fi son ya ji ana karanta surori masu "Hamim" saboda ya riƙa sauraron Saddiqul Minshawi lokacin haddarsa, to idan ana karantawa sai ya riƙa ji kamar yana cikin aljanna.

Iyalina

Ina da mata uku da 'ya'ya takwas, in ji malamin wanda ya ce yana yi wa Allah godiya kan hakan.

Malam ya ce yana son shinkafa da waje dafa duka a irin abincin da ake yi masa a gida.