Ya kamata a daina bai wa Fernandes kyaftin a United - Sutton

Bruno Fernandes

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ya kamata a daina bai wa Bruno Fernandes aikin kyafti, bayan da Liverpool ta ci Manchester United 7-0 in ji Chris Sutton.

Dan kwallon tawagar Portugal, shine kyaftin a wasan na ranar Lahadi, bayan da mai mukamin, Harry Maguire ke zaman benci.

An caccaki Fernandes kan halayyar da ya nuna a wasan na hamayya da Liverpool a gasar Premier League.

''Akwai 'yan wasan da suka fi shi cancanta, wadanda suka kware wajen jaragoranci,'' in ji Sutton

''Fernandes bai da ce da jarorancin United ba, akwai Casemiro ko Raphael Varane duk suna sama da shi a kwarewa da iya shugabanci.''

Shi dai Sutton tsohon dan wasan Premier League ne da ya buga gurbin cin kwallaye.

Fernandes, mai shekara 28 ya ci kwallo 57 ya bayar da 50 a wasa 166 da ya yi wa United.

Dan kwallon tawagar Portugal an dauki bidiyonsa a lokacin da ya ture mataimakin alkalin wasa a minti na 81, koda yake ba a hukunta shi ba, hasali FA ba ta dauki mataki ba, bayan kammala wasan ta ce ba ta ga wani laifi ba.

BBC ta fahmci cewar dan wasan bai ce a sauya shi ba a karshen fafatawar, bayan da wasu ke ganin ya yi alamun a cire shi daga wasan.

An bayar da misali rashin kwazo da ya nuna, bayan da dan wasan Liverpool, Stefan Bajcetic ya wuce shi da kwallo a gefen fili, maimakon ya bi shi sai ya tsaya abinsa.

Liverpool ta ci United mako daya tsakani da kungiyar Old Trafford ta lashe Carabao Cup, na farko da Erik ten Hag ya dauka bayan da ya karbi kungiyar a watan mayu.

United tana ta uku a teburin Premier, za ta buga zagayen quarter finals a FA Cup tana kuma zagayen 'yan 16 a Europa League.

To sai dai dan jarida, Rory Smith ya ce ''Fernades mayaki ne yana kokari sosai a United, kawai wasan ne ya bai wa United ruwa''

Smith ya kara da cewar ''Bruno aka fi sawa ido Casemiro bai taka rawar gani ba, sannan canjin da Ten Hag ya yi ya taba United, wajen kasa yin kwazo.''